Likitocin Najeriya sun fara yajin aikin sai-baba-ta-gani
Likitoci
Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Kasa (NARD) ta tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Litinin.
NARD, wadda gammaya ce ta kungiyoyin likitoci, ta ce za ta dakatar da dukkan ayyukan kula da marasa lafiya, ciki har da na gaggawa da kuma kula da masu coronavirus karfe 12:00 na daren Litinin.
Kungiyar wadda ta sanar da matakin a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta yanke shawarar ne bayan taron da Majalisar Zartarwarta ta gudanar.
- Likitocin Najeriya za su tafi yajin aikin sai baba ta gani
- Likitoci sun ki yarda da rage albashi a Kaduna
Gamayyar kungiyoyin likitocin za ta fara yajin aikin ne saboda rashin isasshen albashi da kuma kayan kariya musamman ga likitocin da ke yaki da cutar coronavirus.
Shugaban NARD, Aliyu Sokomba ya ce gwamnati ta gaza cika sharudan da aka gindaya mata, musamman na kara albashin likitocin da ke cikin barazanar kamuwa da cutar.
Sai da suka yi gargadi a baya
A kwanakin baya dai kungiyar likitocin ta ce yajin aikin ya zama wajibi saboda mawuyacin halin da mambobinta suke ciki.
Shugaban kungiyar wadda ke matsayin uwar kungiyoyin likitocin asibitocin gwamnati ya kuma ce “Yajin aikin namu na sai baba-ta-gani ne.
“Babu wanda zai fito aiki, kama daga masu jinyar masu cutar COVID-19 zuwa masu kula da wasu cututtuka da ke bukatar kulawar gaggawa.
“Mun umarci dukkan likitoci da sauran manyan ma’aikatan lafiya cewa su ma su bi sahu da zarar an fara yajin aikin”, in ji sanarwar.
Kungiyar ta kuma jajanta wa ‘yan Najeriya kan irin halin da za su iya fadawa da zarar ta fara yajin aikin a mako mai zuwa.
Ta kara da yin Allah-wadai da irin halin ko-in-kula da ta ce gwamnati ke nuna wa bangaren lafiya na kasar.
Ta kuma koka kan mawuyacin yanayin aiki da mambobinta ke ciki musamman wadanda ke aiki a cibiyoyin lafiya mallakar jihohi.
Ko a kwanakin baya sai da reshen Babban Birnin Tarayya na kungiyar ya shiga yajin aikin a farkon bullar annobar a Najeriya bisa dalilan kin biyan hakkoki ma’aikatan lafiya.