A yau za a rufe hanyar Lafiya zuwa Akwanga a jihar Nasarawa
Kamfanin China Harbour da ke gyaran hanyar Keffi zuwa Akwanga da kuma Lafiya zuwa Makurdi, ya sanar da cewa yau Litinin 2 ga watan Satumba 2019 za a rufe hanyar wanda zata fara daga nisan kilomita daya daga garin Eggon zuwa Akwanga. Za a dai rufe hanyar ne daga karfe 10 na safe zuwa 5 […]
Kamfanin China Harbour da ke gyaran hanyar Keffi zuwa Akwanga da kuma Lafiya zuwa Makurdi, ya sanar da cewa yau Litinin 2 ga watan Satumba 2019 za a rufe hanyar wanda zata fara daga nisan kilomita daya daga garin Eggon zuwa Akwanga.
Za a dai rufe hanyar ne daga karfe 10 na safe zuwa 5 na yamma don haka za a iya samun cinkoson ababen hawa a yankun da za a gudanar da aikin, aikin ya hada da fadada hanyar zuwa biyu da kuma sabunta hanyoyin.