A yayin da aka rantsar da sababbin shugabannin Gizagawa: Ga Gajeren tambihi ga Gizagawa
A ranar Asabar da ta gabata, Gizagawan Zumunci, kwansu da kwarkwatarsu, sun hadu a zauren taro na Muhammadu Maccido da ke Kwalejin Barewa Zariya, inda aka gudanar da bikin rantsar da shugabannin Gizagawa na kasa da kuma na jihohi. Muhimman iyayen Gizagawa da suka halaci bikin sun hada da Malam Mahmoon Baba Ahmad da Malam […]
A ranar Asabar da ta gabata, Gizagawan Zumunci, kwansu da kwarkwatarsu, sun hadu a zauren taro na Muhammadu Maccido da ke Kwalejin Barewa Zariya, inda aka gudanar da bikin rantsar da shugabannin Gizagawa na kasa da kuma na jihohi. Muhimman iyayen Gizagawa da suka halaci bikin sun hada da Malam Mahmoon Baba Ahmad da Malam Bala Muhammad da Farfesa Yusuf Adamu da Zanwan Lafiyar Bare-Bari da Tafidan Lafiyar Bare-Bari da sauransu da dama. Saboda muhimmancin bikin nan, Gizago ya ga ya kamata ya jaddada wannann tambihi, kamar haka:
***
Assalamu alaikum, Ya ku Gizagawan Zumunci. Wannan lokaci ne mai matukar muhimmanci ga kowane Bagizage da kowace Bagizagiya. Lokaci ne da ya bijiro mana da sababbun al’amura, wadanda suka zama abubuwan kulawa, abubuwan nazari, musamman domin mu waiwaya baya, mu duba matsayin da muke ciki a yanzu, sannan kuma mu hasashi dogon zangon da ke gabanmu. Wadannan sababbin al’amura, na zabi in kasa su zuwa manyan gidaje uku – Sabbin shugabanni, sabuwar tafiya kuma sabuwar akida.
Bari in fara da batu na farko, mai matukar muhimmanci, wato sabbin shugabanni. Kowane Bagizage da Bagizagiya na halal, yana sane da cewa a makon da ya gabata ne aka rantsar da wadannan zaratan Gizagawa a matsayin shugabanni, kamar haka:
1-Sharif Auwal Falala- Shugaba. 2-Malam Auwal L.K- Mataimakin Shugaba. 3-Aliyu Abdullahi danlabaran- Magatakarda. 4-Yusuf Abubakar Zamfara- Mataimakin Magatakarda. 5-Yahaya Usman Maikatifa- Ma’aji. 6-Hajiya Zulai Zaki Jos- Mataimakiyar Ma’aji. 7-Ibrahim Hamisu Kabara- Sakataren. 8-Habu Tsoho Malumfashi-Jami’in Hulda Jama’a. 9-Auwal Tahir Sabongida- Mataimakin Jami’in Hulda Jama’a. 10-Abdullahi Alkwatonawi- Sakataren Tsare-tsare. 11-Musa Baraya Muhammad- Mataimakin Sakataren Tsare-tsare. 12-Muhammad Jungudu- Jami’in Kula da Walwala. 13-Suleman Idris- Mataimakin Jami’in Kula da Walwala. 14-Barister Nuhu Sambo- Mai ba da Shawara a kan Shari’a. 15-Dokta Nasir Muhammad Bauchi- Mai Binciken Kudi.
16-Ibrahim Abubakar- Mataimakin Mai Biciken Kudi. 17-Abubakar Hamisu Yankatsari- Mai Ladabtarwa. 18-Ado Iro Charanci- Mataimakin Mai Ladabtarwa. 19-Hajiya A’isha Lawal Tarauni-Shugabar Mata. 20-Ummu Abdullahi Zariya- Mataimakiyar Shugabar Mata.
Sai kuma shugabannin jihohi da aka rantsar su ma a makon da ya gabata. Duk da cewa ban samu ikon zayyana sunayenku daidai ba, ku yi mini uzuri, domin kuwa kuna da yawa, amma ku sani, ku ne fitilolin da za su haska dukkan jihohinku, sannan ku dunkule waje daya domin haskaka uwar kungiya ta kasa.
Ya ku zaratan shugabannin Gizagawa na jihohi da na kasa baki daya, ina taya ku murna da wannan babbar nasara da kuka samu. Allah Ya taya ku riko.
Bayan haka, ina son in daure ku da jijiyoyin jikinku, domin ku kara nabba’a domin sake dasa muhimmin al’amari a zukatanku. Ku sani, babu abin da ya tara ku kuma ya ba ku wannan kima sai zumunci da amana. Don haka, ku kasance masu kallon kowane al’amari a bagiren zumunci – kowa naku ne, babu wariya, babu bambanci. Haka kuma a kowane lokaci, ku kasance masu adalci a kowane al’amari. Idan kuka yi haka, babu shakka tarihi zai rubuta ku da alkalamin zinari, kuma tarihi zai yi alfahari da ku, daga karshe ku samu lada bisa lada, saboda zumunci da amanar da kuka jaddada kuma kuka gudanar. Allah Ya ba ku ikon aiwatarwa, amin.
Sai kuma mu duba al’amari na biyu – sabuwar tafiya. Ya ku Gizagawan Zumunci, ya kamata mu waiwaya baya, mu gane tasirin haduwarmu a cikin wannan babban al’amari na Gizago. Dukkanmu, al’amari guda ne ya hada mu – zumunci. A can baya, mafi yawanmu ba mu san juna ba, wasu ma ba mu taba haduwa da juna ba, duk kuwa da cewa wasu ma garuruwanmu daya da juna. Ikon Allah da karfin niyyar sada zumunci da shaukin tallafin juna ne suka hada mu cikin wannan zumunci.
Tun da al’amarin haka ne, to kuwa lallai ya dace mu sake jaddada niyya, mu sake gane girma da muhimmancin da ke tattare da wannan zumunci. Don haka, a wannan sabuwar tafiya, lallai ne mu karkade duk wani bakin kuduri da Shaidan ke bijiro mana da shi, mu wanke tunaninmu, mu niyyaci alheri kuma mu jaddada alheri ga junanmu.
Mu kasance tamkar abin da Hausawa ke kira ‘tsintsiya madaurnki daya.’ Mu zama masu shawartar juna da yi wa juna nasiha da hakuri. Mu ba shugabanninmu dukkan kwarin gwiwa da goyon bayan da suke bukata, domin su ja mu zuwa alheri a wanan sabuwar tafiya.
Lallai ne ku sani, ina jinjina muku Gizagawa, ina taya ku murnar zaben da kuka yi na zaratan shugabanni. Allah Ya ba mu ladar zumunci kuma Ya sanya mu ci gaba da kaunatar juna a kodayaushe, amin.
Batu na uku kuma na karshe a jerin maudu’an wannan bayani, shi ne batun sabuwar akida. Ya ku Gizagawa, ku gane, duk wani al’amari na rayuwa da mutum zai yi, ya kamata a ce yana da akida ta musamman da za ta yi masa jagora. Shin ko kun san akidar da ta kamaci kowane Bagizage da Bagizagiya? Koda kun sani, ku kara sani, akidar dai ita ce Zumunci!
Ya kamata ku tuna da takenku: Gizagawa-Zumunci! Zumunci-Gizagawa!!
Idan har kun sani kuma kun amince da wannan akida, to ya zama dole ku san shika-shikan da za su yaukaka kuma su taimaka wajen tafiyar da wannan akida ta Zumunci.
Akidar zumunci ba za ta samu ba sai da gaskiya. Don haka, mu jajirce mu fi karfin Shaidan, mu aiwatar da mu’amala a tsakaninmu da sauran al’umma bisa gaskiya da amana. Mu zama masu kaunar juna a kowane lokaci. Mu cire kwadayi da zalunci a cikin mu’amalarmu da juna. Mu kasance masu taimakon al’umma, mu zama jakadun kirki ga al’ummaru gaba daya. Wannan ita ce akida ta kwarai da ta kamaci kowane Bagizage da Bagizagiya.
Daga karshe, ina mai addu’ar Allah Ya karfafa mana niyya, Allah Ya ba mu ikon jaddada zumunci ga junanmu kuma Ya ba mu dukkan ladar da Ya yi alkawarin ba mai zumunci. Allah Ya yi mana jagora, amin!