A yayin da Jihar Katsina ta cika shekara 30 da kirkirowa

  A ranar Asabar (23-09-2017) ce Jihar Katsina ke cika shekara 30 da kirkirowa, domin kuwa an kirkiro ta ne a zamanin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida tare da Jihar Akwa-Ibom a ranar 23-09-1987 kuma tun daga lokaci nan aka yi ta samun sauye-sauyen gwamnatoci, na soja da na farar hula. Babban makasudin wannan tsokaci, […]

A yayin da Jihar Katsina ta cika shekara 30 da kirkirowa
A yayin da Jihar Katsina ta cika shekara 30 da kirkirowa

 

A ranar Asabar (23-09-2017) ce Jihar Katsina ke cika shekara 30 da kirkirowa, domin kuwa an kirkiro ta ne a zamanin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida tare da Jihar Akwa-Ibom a ranar 23-09-1987 kuma tun daga lokaci nan aka yi ta samun sauye-sauyen gwamnatoci, na soja da na farar hula. Babban makasudin wannan tsokaci, zan yi shi ne da nufin duba muhimman sauye-sauye da ci gaban da aka samu a cikin shekara biyu na mulkin gwamnatin APC, karkashin mulkin Gwamna Aminu Bello Masari.

Da farko dai, a matsayina na dan Jihar Katsina kuma wanda ke kula da yadda al’amuran yau da kullum ke gudana a jihar, tun daga samun jiha a 1997, babu shakka mun ga yadda gwamnatoci daban-daban suka gudanar da mulkinsu a jihar; tun daga kan mulkin sojoji har zuwa dawowar mulkin dimokuradiyya. Don haka irin yadda mulki ke gudana a jihar, a hannun kwararren dan siyasa, Dallatun Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, lallai abin dubawa ne.

A gwamnatocin baya, idan muka yi la’akari da yadda rayuwar ’yan fansho ta kasance, abin akwai takaici. Kamar yadda al’amuran suka kasance, za ka ga mutum ya yi ritaya, amma ya dauki lokaci ba a biya shi hakkokinsa ba. Wasu kuma idan an zo biyansu, ana yi masu kwange.

A halin da ake ciki, ’yan fansho a Jihar Katsina sai son barka, domin kuwa an biya su basussukansu da wasu ke bi tun tsawon shekara takwas kuma an ci gaba da biyan wadanda ke kai a yanzu.

Idan aka zo batun rashin aikin yi da zaman kashe wando da matasa suka samu kansu a Jihar Katsina a tsarin gwamnatocin da suka gabaci ta Masari, abin bai da dadin ji. An wayi gari matasa babu abin da suke yi, daga shaye-shaye sai munanan ayyukan sara-suka. Lokacin da Masari ya samu mulki, ya yi katatun-ta-natsu, inda ya dauki niyyar ceto matasa daga ragaita. Wannan ya sanya ya kirkiro da ingantattun hanyoyin tallafa masu, musamman wajen koya masu sana’o’in hannu, tare da karfafa masu gwiwa da jari da kuma kayan aikin sana’o’in da suka koya. Wannan ya sanya a karon farko, aka yaye matasa sama da 700, aka ba su jari, sannan aka kara dibar wasu. Kamar yadda rahotanni suka bayyana, haka tsarin abin zai ci gaba har zuwa inda Allah Ya nufa.

A ta bangaren karfafa wa mata kuwa domin su samu sana’o’i’, an rika rarraba wa kungiyoyin gama kai na mata dabbobin kiwo, wasu kuma aka rika ba su jarin gudanar da kananan sana’o’i a gida, domin tallafa wa iyalai. Irin wannan tsari, ba a san shi ba a gwamnatocin baya, a Jihar Katsina.

Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin Arewa da aka bari baya ta fuskar kasuwanci. A zuwan Gwamnatin Masari, an samu ci gaba wajen karfafa ’yan kasuwa ta hanyoyi da dama. Ga masu burin gina kanana da matsakaitun kamfanoni, an tallafa masu da rancen kudi ba tare da ruwa ba. An gina shagunan ’yan kasuwa a sassa daban-daban na jihar, domin habaka kasuwanci.

Harkokin kungiyoyin gama kai na da muhimmanci ga kowace al’umma. A wannan janibi, an shigo da tsare-tsare masu muhimmanci na wayar da kai ta koya masu ayyukan ci gaban al’umma.

Ta bangaren addini kuwa, ganin yadda yake da tasiri sosai wajen jagorancin rayuwar al’umma, Gwamnatin Masari ta dauki hanyoyi masu bullewa wajen tallafa wa kungiyoyin addini daidai gwargwado, ba tare da nuna bambanci ba. Gwamnati ta inganta Ma’aikatar Al’amuran Alhazai, domin dawainiyar maniyyata da kyautata jin dadinsu a gabanin tafiya da lokacin isar su Saudiyya har zuwa dawowarsu.

A bangaren ilimi kuwa, nan ma abin akwai bukatar dubawa da nazari. A can baya kafin zuwan Masari, an samu tabarbarewar harkokin ilimi. Akwai karancin azuzuwa a makarantu da karancin kayan aiki, kamar kuma yadda ake da karancin kwararrun malamai. Wadannan matsaloli da wasunsu, sun haddasa dalibai na faduwa jarabawar karshe ta sakandare, duk kuwa da cewa ana kashe kudade masu yawa a fannin. Domin shawo kan wadannan matsaloli, gwamnati ta dauki matakai daban-daban. Cikin matakan, sun hada da gyaran makarantun firamare da na sakandare sama da 2000 a sassa daban-daban na jihar, kuma ana ci gaba da gina wasu isassun azuzuwa da sama masu kayan zama na tebura da kujeru da sauransu. A kwanan nan kuma gwamnatin ke yunkurin daukar malaman makarantar fimare masu yawa, domin magance karancin malamai da ake fama da shi.

Idan muka tuntubi bangaren kiwon lafiya. An gyara tare da inganta gine-ginen asibitocin manyan garuruwan jihar, musamman ma Katsina, Daura, Malumfashi, Funtuwa da Kankiya. Haka kuma an dauki matakan sama masu kayan aiki na zamani kuma masu inganci.

Harkar noma da kiwo na daga cikin manyan sana’o’in da ake bugun gaba da su a Jihar Katsina. Don haka manoma da makiyaya na da bukatar tallafi da kulawa daga gwamnati. Dalili ke nan aka samar da kayan noma, ma’ana na’urori da motocin noma na zamani ga manya da matsakaita da kananan manoma a jihar. Wannan ya sanya aka maida hankali wajen tallafar noman rani a sassa daban-daban na jihar. Musamman a kwanakin baya ma aka kaddamar da aikin noman shinkafa a yankin Sabke. A daminar bara, an shigo da ingantaccen tsarin raba takin zamani, wanda aka raba daidai gwargwado, manoma suka samu ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba. An gyara madatsun ruwa da ake da su a jihar, musamman ma madatsun ruwa na Jibiya da Ajiwa da Safke saboda samar da ruwan sha da noman rani da sauran muradu.

An gudanar da aikin hanyoyi a wurare daban-daban, kamar wasu kauyuka a Safana, Batsari, suka hada da Dutsen-ma da wasu kauyuka a karamar Hukumar kafur da wurare da dama. An gina tare da gyara hanyoyin ruwa cikin birane da kauyuka, musamman nan cikin garin Katsina, inda ruwan damina ya fi wa barna. Haka kuma, an dauki matakan tsabatace manyan biranenmu baki dayansu da kawar da kazanta a bakin hanya da yashe kwatoci.

Ta fuskar tsaro a fadin jihar baki daya, gwamnati ta taka rawa, musamman kananan hukumomin Jibiya, Batsari, Safana, danmusa, kankara, Faskari, dandume da Sabuwa. Wani babban aiki da aka yi nasara, shi ne na sasantawa da yin sulhu da barayin shanu a fadin jihar baki daya, inda suka mika makamansu ga hukuma. Wannan ya yi tasiri, inda aka kawo karshen fada tsakanin makiyaya da manoma.

A yadda al’amura ke gudana a hukumance a Jihar Katsina, madamar aka ci gaba a haka, babu shakka za a samu gagarumin ci gaba a cikin al’umma. Babu shakka tsarin yadda mulkin Gwamna Masari ke tafiya, sai dai a ce Allah san barka!

Muhammad Mustapha (08058538165), ya rubuto daga Katsina