A yayin da Kano ke kokarin kwato hikimar da ta bace

Kokarin da Gwamnatin Jihar Kano ke yi na dawo da wasu daga cikin tsofaffin tsarin tsaro na lardi zuwa yanayin tsaro na zamani saboda magance matsalolin tsaro yana da muhimmanci. An amince a yi amfani da tsarin ne a wani babban taron Majalisar Tsaro ta Jihar da aka yi makon jiya a tsakanin gwamnatin jihar […]

A yayin da Kano ke kokarin kwato hikimar da ta bace
A yayin da Kano ke kokarin kwato hikimar da ta bace

Kokarin da Gwamnatin Jihar Kano ke yi na dawo da wasu daga cikin tsofaffin tsarin tsaro na lardi zuwa yanayin tsaro na zamani saboda magance matsalolin tsaro yana da muhimmanci. An amince a yi amfani da tsarin ne a wani babban taron Majalisar Tsaro ta Jihar da aka yi makon jiya a tsakanin gwamnatin jihar da Masarautar Kano. Rahotanni sun ce Gwamnatin Jihar Kano ta dawo da tsarin ne domin ta sanya masarautu cikin harkar samar da zaman lafiya a jihar.

Da yake bayyana sabon tsarin, Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II ya ce an sanya masarautu cikin tsarin tsaron jihar ne saboda yadda jihohi masu makwabtaka da Kano suke fama da matsalolin tsaro. “Kuna sane da yadda makwabtanmu suke fama da matsalolin tsaro, kuma masu hikima sukan yi rigakafi ne kafin cuta ta sauko musu. Don haka muke bukatar mu zauna cikin shiri.” Sarkin ya kara da cewa, “Hausawa suna cewa idan gemun dan uwanka ya kama da wuta, sai ka shafa wa naka ruwa.” Sarkin ya ce a sabon tsarin, dagatai da hakimai da malamai da kuma masarauta duk za su shiga cikin tsarin samar da tsaro a garuruwansu.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya kira babban taron wanda ya kunshi jami’an DSS da ’yan sanda da sojoji da sauransu. Muna maraba da wannan kokari na Gwamnatin Jihar Kano da masarautar na kokarin fadada harkokin tsaron Najeriya domin magance matsalolin da kasar ke fuskanta. Masarautu suna da matukar muhimmanci wajen samar da zaman lafiya da tattara bayanan abubuwan da suke jawo rikici. Don haka wannan kokari yana da matukar muhimmanci a daidai wannan lokaci da muke fama da matsalolin tsaro, musamman bisa la’akari da yadda sarakuna suke kokarin magancewa tare da sulhu tsakanin mutane da kuma yadda suke kusa da talakawa. Mun yi imani cewa sanya sarakuna cikin wannan tsarin zai taimaka matuka wajen samar da ingantaccen tsaro.

Rashin tsaron da muke fama da shi a Najeriya yanzu bai rasa nasaba da yadda aka mayar da sarakuna baya da kuma yadda aka kwace karfin ikon da suke da shi a karkashin shirin yi wa kananan hukomomi garambawul a 1967 da 1971 da 1976, inda aka fitar da kundin tsarin 1979. Da sannu wadannan gya-gyaren da aka yi suka kwace wa sarakuna karfin ikon a kan ’yan sanda da gidan yari da kotu, aka mayar da su karkashin kulawar Gwamnatin Tarayya da jihohi. Sannan aka soke tsarin gwamnatin lardi aka maye gurbinsa da kananan hukumomi.

Wadannan gya-gyare da aka yi, akalla sun mayar da hannun agogo baya. Tsarin ya sanya karfin ikon masarautu na lura tare da sanin mutanen da suke zirga-zirga ko harkoki a yankunansu ya lalace. Don haka kokarin da Jihar Kano ke yi na dawo da sarakuna cikin tsarin tsaro abin a yaba ne matuka. Wannan ba wai kokarin tuna baya ba ne kawai, wannan wani shiri ne da ya kamata a kalla a matsayin gyara harkokin tsaro da ya tabarbare a yanzu.

Bai kamata mu yi watsi da sarakuna ba a kokarinmu na samar da zaman lafiya da tsaro. Ya kamata a yi amfani da su sosai wajen samar da zaman lafiya ta hanyar tattara bayanai. Matsalolin da muke fama da su yanzu yawancin akwai su a da. Don haka ya kamata ne mu yi amfani da yadda sarakunan suka bi wajen magance su a da. Sannan muna kira da sauran jihohin Arewa da suke makwabtaka da Kano su ma su yi irin wannan tsari.

Har yanzu ana muhawara a kan ko a sanya sarakuna cikin kundin tsarin mulki kasa, amma bangaren da kasar ke matukar bukatar taimakon sarakunan a yanzu shi ne tsaro. Sarakuna sun fi kowa cancanta su gane tare da bankado duk wani mara ji da ’yan daba da inda suke boyewa da kuma bankado kungiyoyin da suke barazana ga zaman lafiya lura da yanayin kusancinsu da mutane kafin jami’an tsaro su shigo lamarin. Lallai yanzu ne lokacin da ya kamata mu yi amfani da wannan tsari.