A yayin da likitoci ke kaurace wa Jihar Kogi

Batun nan da aka dade ana yi dangane da rashin biyan ma’aikata albashi a kan kari da rashin tallafi ko dadadawa ga ma’aikata a Jihar Kogi ya kara fitowa sarari, inda a makon jiya aka samu rahoton cewa likitoci har  88 ne suka bar aiki a jihar tun daga lokacin da Gwamnatin Yahaya Bello ta […]

A yayin da likitoci ke kaurace wa Jihar Kogi
A yayin da likitoci ke kaurace wa Jihar Kogi

Batun nan da aka dade ana yi dangane da rashin biyan ma’aikata albashi a kan kari da rashin tallafi ko dadadawa ga ma’aikata a Jihar Kogi ya kara fitowa sarari, inda a makon jiya aka samu rahoton cewa likitoci har  88 ne suka bar aiki a jihar tun daga lokacin da Gwamnatin Yahaya Bello ta kama aiki zuwa yau. Wannan batu an jiyo shi ne daga bakin Shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya, reshen Jihar Kogi, Dokta Kabiru Zubair, a wani jawabi da ya gabatar domin taya Gwamnan murnar cika shekara uku a gadon mulki, inda kuma ya roki Gwamnan ya dauki matakan da suka dace domin gyara al’amura don hana sauran likitocin zurarewa daga jihar.

Zubair ya ce “A karkashin wannan gwamnati, likitoci 88 suka bar aiki a Jihar Kogi, wato 79 da farko sai kuma wadansu 9 da suka bari a kwanan nan.” Ya kara da cewa likitoci da sauran ma’aikatan lafiya su ne jigogin tafiyar da al’amuran kiwon lafiya a ko’ina a duniya. “A biya basussukan albashin watannin baya ga likitoci da sauran ma’aikatan lafiya, a fara biyan sabon tsarin albashi na CONMESS, a kara wa wadanda suka cancanta girma da kuma karin matakin albashi da ake yi duk shekara, wadannan matakan da ma wasu za su iya magance wannan matsala da ba ta d  dadin ji,” inji shi.

Bayan kwanaki kadan da batun, sai Gwamnatin Jihar Kogi ta amince wa Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar da ke Lakwaja ta dauki sababbin likitoci da za su maye guraben wadancan da suka bar aiki. Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Haruna Saka ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne da nufin magance matsalar likitocin da ke barin aiki a jihar. Ya ce tuni aka ba Asibitin Kwararru na Jihar  ikon shirya kwasa-kwasai don koyar da likitoci, inda za su samu dukan kayayyakin koyar da likitoci don su kware, su zama cikakkun likitoci masu lasisi. Ya ce tuni Gwamna ya shirya musu kwarya-kwaryar kabakin kyautata rayuwar aiki da ta hada da bashi marar ruwa da sauransu.

Dangane da batun zurarewar da likitoci suke yi daga aiki a jihar, Dokta Saka ya ce wannan ba wani abin mamaki ba ne, kasancewar a duk lokacin da Gwamnatin Tarayya ta bude hanyar daukar ma’aikata, likitoci kan bar jihohi su yi kokarin komawa can.

Wannan abin takaici ne a ce likitoci na barin aiki a jiha saboda matsalolin rashin biyan albashi ko rashin kyakkyawan yanayin aiki, duk kuwa da cewa dama can ana karancinsu. Jihar Kogi dai ta yi kaurin suna a bangaren rashin biyan albashi ga ma’aikatanta, duk da cewa ta amshi tallafin “Paris Club” daga Gwamnatin Tarayya. Wannan matakin da likitoci suka dauka na barin aiki a Jihar Kogi, wata manuniya ce kawai ga sauran ma’aikata a jihar da ke nuna cewa an bude musu hanya kawai. Al’umma da yawa dai sun dogara ne da asibitocin gwamnati a jihar, kuma ga shi dama likitocin da ke asibitocin ba su wadata ba. Yanzu kuma a ce  likitoci har 88 sun bar aiki a jihar, wannan babbar musiba ce ga al’ummar jihar.

Gaskiya matakin da Gwamnatin Jihar Kogi ta dauka a kan wannan matsala abin takaici ne, domin da farko ma ba ta damu da batun ba har sai da Kungiyar Likitoci a jihar ta daga murya, ta koka kan lamarin. Ya zama wajibi a inganta albashin ma’aikatan lafiya a jihar, a kuma tanadar musu wasu abubuwan kyautatawa, yadda za su ji dadin zuwa aiki a jihar. Gwamna Yahaya Bello, ya zama wajibi ya dauki matakin gaggawa na inganta albashin daukacin ma’aikatan jihar da biyansu a kan lokaci, ba ma kawai na ma’aikatan lafiya ba. Idan kuwa ba a dauki matakin gyara da ya dace ba, to ba ma’aikatan lafiya kadai ba, za a wayi gari sauran sassan ma’aikata sun ajiye aiki a jihar, wanda hakan bai kamata a bari ya faru ba.