A yayin da mata ’Yan Najeriya 26 suka halaka a teku
A kullum yaumin ana samun labarai marasa dadi game da ’yan Najeriya da sauran ’yan kasashen Afrika ta Yamma da kuma wasu al’ummun da yaki ya tagayyara a kasashen Gabas ta Tsakiya, musamman yadda suke shiga cikin matsaloli daban-daban kamar nitsewa a teku, a yayin ketarawa zuwa kasashen Turai. Sai dai labarin baya-bayan nan, inda […]
A kullum yaumin ana samun labarai marasa dadi game da ’yan Najeriya da sauran ’yan kasashen Afrika ta Yamma da kuma wasu al’ummun da yaki ya tagayyara a kasashen Gabas ta Tsakiya, musamman yadda suke shiga cikin matsaloli daban-daban kamar nitsewa a teku, a yayin ketarawa zuwa kasashen Turai. Sai dai labarin baya-bayan nan, inda budare ’yan Najeriya, ’yan kimanin shekara 14 zuwa 18 da aka samu a mace, a cikin jirgin ruwan kasar Sifen, ya bude sabon shafin takaici, na yadda ake samun masu ketarawa zuwa Turai ta haramtacciyar hanya.
Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, an yi lalata da matan ne sannan aka kashe su a tekun Meditareniya, a lokacin da suke kokarin tafiya Turai. Daga bisani ne aka gano gawarwakinsu a cikin wani jirgin ruwan yaki na kasar Sifen mai suna ‘Cantabria’ wanda yake dauke da ’yan hijira 375 tare da gawarwakin mata 23. Kamar yadda kafafen watsa labarai na kasar Italiya suka bayyana, an adana gawarwakin ne a wani gidan kankara na bangaren jirgin. Sun kara da cewa mafi yawa daga wadanda suka tsira a jirgin su 375 ’yan Afrika ne da suka fito daga bangaren Sahara, musamman daga Najeriya, Senegal, Ghana da Gambiya da Sudan. Daga cikin wadanda suka tsira, akwai mata 90, wadanda 8 daga cikinsu duk suna dauke da ciki, akwai yara 52, tare da wasu maza da mata ’yan kasar Libya. Tuni dai aka ce jami’an tsaro na kasar Italiya suka fara binciken al’amarin.
Shekaru da dama a baya, haka al’amarin ke kasancewa, inda ’yan Najeriya kan hau dokin kasada su fantsama cikin Hamadar Sahara zuwa kasar Libya, ta hanyar taimakon tawagogin ’yan sumoga. Wasu da dama sun rasa rayukansu saboda wahala da yunwa da kishi kuma wadanda ma suka samu nasarar isa Libya, sukan fuskanci kalubalen tafiyar da rayuwarsu cikin kaskancin bauta, bayar da cin hanci, kamar kuma yadda ake nuna masu wariya da kabilanci daga masu gudanar da wannan sana’a da jami’an tsaro, domin dai su tsallakar da su zuwa Turai domin samun abin duniya, ta kogin Meditereniya.
Da dama daga cikinsu kan kwashe watanni ko shekaru a Libya, inda wasu kan fada kurkuku, zaman jarun, wasu ma a kashe su gaba daya a wannan kasa da rikice-rikice suka yi wa katutu. ’Ya uwansu ba za su iya gano su ba ko su san abin da suke ciki har abada. Suna daukar wannan kasada ne saboda sun kudurce a zukatansu cewa Turai wata Aljannar duniya ce, alhali ba su san cewa duk da irin matsalolin da ke akwai a Najeriya, rayuwa ta fi sauki fiye da can ba, musamman idan aka kwatanta kunci da hadarin da suke fuskanta a hanyar zuwa Turai ta haramtattar hanya.
Ya kamata ya zuwa yanzu, iyayen da ke tura ’ya’yansu mata zuwa Turai su fahimta da cewa karuwanci ’ya’yansu ke zuwa yi a can. Abin da kuma ba su sani ba shi ne, baya ga karuwanci, suna gudanar da rayuwarsu ne cikin kaskanci da wulakanci da bakar wahala, inda daga karshe kuma a rasa biyan bukata. Akwai bayanin da ke nuna cewa ’yan sumoga da ke shigar da mutane Turai ta barauniyar hanya, suna amsar kudi, kimanin Dala 6000 daga hannun duk mutum daya, wanda haka ke sanya alamar tambayar cewa, shin anya talauci ne ke sanya mutum tafiya Turai, alhali ya mallaki wadannan kudi? Idan ba hadama ba, wanda ya mallaki wadannan adadin kudi a Najeriya, ai sun ishe shi jalin da zai yi sana’a mai halacci a gida kuma ya samu alheri hankali kwance, cikin iyalinsa, ’yan uwa da abokan arziki.
Duk da cewa gwamnati tana kokarin dakile wannan al’amari na safarar mutane, musamman yadda ta kafa Hukumar Yaki Da Safarar Mutane (NAPTIP) a 2003, har yanzu akwai sauran aiki a gabanta. Ya kamata Hukumar Wayar Da Kan Jama’a (NOA) ta shigo cikin batun, yadda za ta rika kwarmata illolin da ke tattare da wannan kasada, domin al’umma su ida fahimta. Ya kamata kuma iyayen da ke tura ’ya’yansu zuwa Turai ta wadannan hanyoyi su sake tunani, su shafa wa kansu lafiya. Haka kuma Gwamnatin Najeriya ya kamata ta hada hannu da ta Jamhuriyyar Nijar, domin dakile ’yan sumoga masu safarar mutane zuwa Turai. Haka kuma ya dace gwamnatocin Afrika su inganta tattalin arzikin kasashensu da fito da hanyoyin saukaka sana’a da samar da aikin yi ga al’umma, wanda haka zai rage hakilon da matasa ke yi na fita waje domin neman rayuwa mai sauki.