A yayin da Shekarau ya bar wa Kwankwaso PDP

Bayan shafe sama da wata guda kan muhawarar da al’ummar Jihar Kano ke yi a kan yadda makomar tsohon Gwamnan Jihar, Malam Ibrahim Shekarau za ta kasance idan har ya canja sheka daga PDP, saboda sabon salon siyasar da za a gara a jihar bayan da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya canja […]

A yayin da Shekarau ya bar wa Kwankwaso PDP
A yayin da Shekarau ya bar wa Kwankwaso PDP

Bayan shafe sama da wata guda kan muhawarar da al’ummar Jihar Kano ke yi a kan yadda makomar tsohon Gwamnan Jihar, Malam Ibrahim Shekarau za ta kasance idan har ya canja sheka daga PDP, saboda sabon salon siyasar da za a gara a jihar bayan da tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya canja sheka daga APC zuwa PDP. 

A ranar Asabar 8 ga Satumba, Malam Shekarau ya sanar da daruruwan magoya bayansa a wani taro da ya kira a gidansa da ke Kano cewa ya fice daga PDP, ya kuma koma APC, jam’iyyar da yake daya daga cikin mutum uku da suka jagoranci kafa ta a shekarar 2013.

Malam Shekarau ya fada musu cewa babban dalilin da ya sa ya fice daga  PDP ya koma APC, bai wuce abin da ya kira rashin adalcin da shugabancin PDP na kasa ya yi musu ba. Yana mai kafa hujja da rushe kwamitin zartaswar jam’iyyar a Kano ba gaira ba dalili. Sannan da kin bin umarnin wata babbar kotu a jihar da bayan sauraren karar da wadansu ’ya’yan jam’iyyar suka kai uwar jam’iyyar ta kasa, suna kalubalantarta bisa yunkurin rushe shugabancin kwamitin zartarwa na jihar, alhalin babu wani laifi da suka yi da ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar. 

“Duk da waccan kotu ta ba da umarnin cewa kowa ya tsaya a matsayinsa har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci, sai kwatsam PDP ta kasa karkashin jagorancin Uche Secondus, ta sa kafa ta shure umarnin kotu, tare da nada kwamitin rikon kwarya mai wakilai 7, daga cikinsu kuma 5, daga bangaren Kwankwasiyya suka fito, alhali ni da Alhaji Aminu Wali ke rike da jam’iyya shekara da shekaru lokacin da mutane irin su Kwankwaso suka fice daga PDP, aka ba mu wakilai biyu rak. Irin wadannan dalilai da makamantansu da kokarin da muka rika yi ni da Aminu Wali wajen ganin Kwankwaso ko PDP ta kasa sun saurare mu, don kawo maslaha, amma abin ya ci tura, don haka ni da magoya bayana ban ga wurin zama ba a cikin PDP don kuwa ba za a yi mana adalci ba.” 

Kodayake Malam Shekarau bai zargi Kwankwaso da laifi wurin canjin shekar tasa ba, bisa abin da ya ce a zamansu na mutum da mutum ba ya da wata matsala tsakaninsa da Kwankwaso da za ta hana su shan inuwar siyasa daya. Amma dai masu kula da al’amuran yau da kullum sun yi hasashen cewa dole ne Shekarau ya bar PDP muddin Kwankwaso ya dawo cikinta, kamar yadda ta faru a 2014, lokacin da Kwankwason ya baro PDP shi da gwamnoni hudu, suka koma APC. 

Haka a wannan fili, ranar 27 ga Maris, 2018, mai taken: “Bulaguron Sanata Kwankwaso zuwa APC,” na yi hasashen cewa ba za a taba zama inuwar siyasa daya a tsakanin Shekarau da Kwankwaso ba, kasancewar a shekarar 2013, Kwankwason ya canja sheka daga PDP zuwa APC, kuma APC ta damka masa shugabancin jam’iyya ta jiha. Na yi wancan hasashe ne bisa ga irin yadda na san zaman doya da manjan da suka yi tun a shekarar 2002, lokacin da Shekarau yake Babban Sakatare a Gwamnatin Kwankwaso, kuma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar neman Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar ANPP a lokacin, takarar daga karshe ya samu nasarar kada Gwamna Kwankwaso na PDP mai mulki. 

To, yanzu ga Shekarau ya dawo APC, jam’iyyar da ya ce bai dawo da wani sharadi nasa ko wasu magoya bayansa ba a kan ba su kowane irin mukami. Amma jama’a sun ci gaba da hasashen cewa za a ba shi takarar kujerer Majalisar Dattawa ta Kano ta Tsakiya, sauran magoya bayansa kuma za a ba su takarar wasu mukamai da suka hada da ’yan Majalisar Wakilai da ’yan Majalisar Dokoki ta jiha da sauransu. 

Sai kuwa hasashen ta tabbata, inda aka bai wa Shekarau damar tsayawa takarar Majalisar Dattawa daga Kano ta Tsakiya. Domin kuwa babban abin da ke gaban Gwamnatin Ganduje a halin yanzu bai wuce yadda za ta samu nasarar sake ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2023 ba, kamar yadda shi kuma Kwankwaso babu babban abin da ke gabansa koda ya gaza cimma burinsa na takarar Shugaban kasa, bai wuce ya ga keyar Gwamna Ganduje a kasa ba. Don haka yanzu ba zai zama abin mamaki ba da Gwamna Ganduje ya yi tayin ba bangaren Shekaran wasu mukamai, kasancewar ya san a siyasar Kano har gobe Malam Shekarau yana da tasiri. Da wannan za ka iya cewa karin maganar Bahaushe “Sai wani ya mutu wani yakan samu.” Sai mu yi fatan Allah Ya nuna mana yadda za ta kaya cikin alherinSa.

Mai karatu bari in kawo maka wani martani da na samu daga wani mai karatu Malam Abdullahi Labaran a kan makalata ta ranar 24 ga Agusta, 2018, lokacin da na tafi aikin Hajj kuma ban samu lokacin dubawa ba sai bayan da na dawo. Ga martanin kamar haka: 

“Malam Ado, idan za ka yi rubutu ka rika jin tsoron Allah a matsayinka na tsohon dan jarida, ka rika binciken jama’a kafin ka furta ko ka gaya wa duniya. Abin da ka fada a kan ’yan Majalisar Jihar Sakkwato karya kake yi babu wani dan Majalisar Dokoki cikin 18, da ke tare da Tambuwal da ke tattaunawa da Wammako, hasali ma yanzu da nake wannan rubutu Wammako na Sakkwato, Tambuwal na kasar Saudiyya tare da wadancan ’yan majalisa 18. To Ado ina ka samu wannan labari na karya? Ka ji tsoron Allah don dan abin da za a ba ka kana sharara karya, kana da ’ya’ya da mata da surukai amma ka bige da karya. Allah Ka shirye mu.”

Na so in yi dogon bayani a kan wannan zargi na Malam Labaran, amma a takaice ina son shi da duk wani mai sha’awar abin da na rubuta ya koma a wancan jarida. Bincike na yi irin namu na ’yan jarida daga wadansu da suka san abin da ke kaiwa da komowa a siyasar Jihar Sakkwato, sannan kuma ai cewa na yi an ce, kamar yadda aikin ya gada. Kuma me Malam Labaran ya ke ci na ba ka ke zuba, ya bari mana ya ga yadda za ta kaya a fagen siyasar jihar, daga nan zuwa lokacin da za a kammala zabubbukan fitar da ’yan takarar kowace jam’iyya don zaben 2019. A kan zargin Malam Labaran na cewa wai ko don dan abin da za a ba ni nake sharara karya. Na ji dadi da ba cewa ya yi an ba ni ba. Duk kuma dan jarida da ya amsa sunansa ba ka raba shi da samun irin wannan zargi sai dai ni ma in ce Allah Ka shirye mu.