A yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kama ragama

A yau Juma’a 29 ga watan Mayu, 2015 wadda ta yi daidai da 10 ga Sha’aban, 1436 BH; Allah cikin ikonSa da hikimarSa Ya hukunta Muhammadu Buhari ya amshi ragamar mulki daga Goodluck Ebele Jonathan. Babu shakka sabon Shugaban kasar ya amshi mulkin a yayin da Najeriya ke fuskantar manyan kalubale masu yawa. Wannan tsokaci […]

A yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kama ragama
A yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kama ragama

A yau Juma’a 29 ga watan Mayu, 2015 wadda ta yi daidai da 10 ga Sha’aban, 1436 BH; Allah cikin ikonSa da hikimarSa Ya hukunta Muhammadu Buhari ya amshi ragamar mulki daga Goodluck Ebele Jonathan. Babu shakka sabon Shugaban kasar ya amshi mulkin a yayin da Najeriya ke fuskantar manyan kalubale masu yawa. Wannan tsokaci zai karkata ne wajen sharar hanya da matashiya da shawara ga Shugaba Buhari da kuma ’yan kasa gaba daya:

Yanayin Najeriya: Babu raba daya biyu, duk wanda ya kwana a kasar nan kuma yake bin al’amuran da ke wakana, ya kwana da sanin yadda Najeriya ta kasance a wannan lokaci. kasa ce wadda a takaice za a iya cewa ta durkushe, sai dai dan abin da ba a rasa ba. Duk wani al’amari wanda yake jigo ne a tafiyar da kasa ya sakwarkwace.
Idan muka duba al’amarin tsaro, kusan babu shi, domin kuwa baya ga illar kashe-kashen al’umma da ’yan Boko Haram suka dade suna yi, haka ma a kudancin kasar nan ake da ta’addancin masu satar mutane suna garkuwa da su domin amsar kudin fansa. Haka kuma kasar ta rikice da sace-sace da fashi da makami, musamman ma satar dabbobin makiyaya da ya ta’azzara. Maganar fyade da safarar mata kuwa sun zama ruwan dare. Kashe-mu-raba, cin hanci da rashawa, almundahana da dukiyar gwamnati kuwa ya zama ado.
Harkar ilimi ta yi raga-raga. A yau ba sai gobe ba, daliban Najeriya suna tafiya kananan kasashe kamar Nijar, Ghana da Uganda domin neman ilimi. A nan gida Najeriya kuwa, saboda rashin ingancin harkar ilimi, dalibai kadan ne ke samun sakamakon jarabawa mai kyau. Makarantu sun lalace, babu kwararrun malamai, babu kayan aiki, babu albashi mai kyau. An samu lokacin da gaba daya jami’o’in kasar nan suka kasance a rufe na kusan shekara daya saboda yajin aiki.
Idan ka dawo kan al’amuran rayuwa kuwa, abin sai dai a ce la haula wala kuwwata. Asibitoci sun zama wuraren aje gawa, babu magani, babu isassu ko kwararrun likitoci, babu kayan aiki. Fannin kasuwanci kuwa, Najeriya ta zama kamar bola wajen tara tarkacen kasashen waje, inda daidai da abin sakacen hakori daga waje ake shigo da shi. Masana’antun cikin gida, kashi 90 cikin dari duk a rufe suke. Harkar noma kuwa ta zama abin tausayi, inda manomi kan sayi taki da matsananciyar tsada, amma abin da yake nomawa kuma a bar shi a wulakance. A takaice, al’amura dai sun yi tabarbarewar da ta wuce misali, wani sauki sai wurin Allah!
Yanayin ’yan Najeriya: Al’ummar Najeriya a wannan lokaci sun kasance tamkar suna zaman ’yan marina, domin kuwa an rarraba kan al’umma. Saboda su cin ma wani karkataccen buri nasu, wasu mutane sun yi uwa kuma suka yi makarbiya wajen cusa gaba da kiyayya tsakanin al’ummar kasa. A yau, an raba kan ’yan Najeriya ta hanyar bangaranci, bambancin addini da na kabila. Tarbiyyar matasa, maza da mata, kai har ma da ta wasu dattawan ta lalace. Ana fama da rashin gaskiya, rashin adalci, yaudara da son kai, ga uwa uba rashin kishin kasa. Al’ummar Najeriya a wannan lokacin sun kasance masu karya doka kai tsaye.
Abin da Shgaba Buhari ya kamata ya yi: A yayin da aka rantsar da Shugaba Buhari a yau, lallai ne ya tsaya kai da fata, ya jajirce kamar yadda aka san shi wajen tunkarar kawo gyara wurjanjan. Kamata ya yi ya tsaya kan muhimman alkawuran da ya yi wa al’umma, wadanda ba su wuce uku ba zuwa hudu. A can baya, ya sha bayyana cewa zai tunkari magance matsalar 1-tsaro, 2-bunkasa harkar noma domin samar da aikin yi da inganta tattalin arzikin kasa, 3-maida hankali wajen hako ma’adinan karkashin kasa da kuma 4-yaki da satar dukiyar al’umma, wanda ya hada da yaki da rashawa da cin hanci.
Ta fuskar tsaro, lallai ne Shugaba Buhari ya nuna jan ido, ya dawo da martabar dukkan sassan ma’aikatun tsaro, wadanda suka hada da soja, ’yan sanda, kwastam da sauransu. A samu zaratan shugabanni masu gaskiya da kishin kasa a nada su domin su jagoranci ma’aikatun tsaron. Ta haka ne za a samu shuagbancin rundunonin mai kyau kuma mai dacewa.
Ta fuskar bunkasa noma kuwa, lallai ne a yi da gaske. A sama wa manoma na gaskiya kayan noma, wadanda suka hada da takin zamani, wadatacce kuma mai rahusa. A samar da hanyoyin ba manoma na gaskiya rancen kudi marar ruwa. Idan sun noma kayan, ya kamata gwamnati ta saya, sannan ta samar da ingantattun hanyoyin da za su yi daraja. Ta hanyar noma kadai, za a iya bunkasa kasar nan da abinci, sannan a magance zaman banza, kamar kuma yadda za a samar da kudin shiga fiye ma da abin da fetur ke samarwa.
Ta fuskar hako ma’adanai kuwa, nan ma abu ne mai kyau, domin kuwa a baya gwamnati ta fi mayar da hankali ne kawai kan man fetur. Shi kuma man fetur a yanzu kadarinsa ya kare a duniya, inda ake sayar da danyen man kasa da dala sittin. Yadda Allah Ya hore wa Najeriya ma’adinai masu yawa a kasa, idan aka maida hankali a kansu, za a mance ma da wani abu man fetur, domin ta nan dukiya za ta rika bubbugowa kuma a ririta ta wajen bunkasa kasa.
Batun yaki da satar dukiyar kasa kuwa, nan ma aiki ne mai matukar muhimmanci kuma mai wahala, amma duk da haka, idan aka inganta jami’an tsaro da kayan aiki, aka biya su albashi mai kyau, aka kuma samar da yanayi mai kyau a sassa daban-daban na rayuwar al’umma, babu shakka za a magance ko a rage shi. Ya zama wajibi a bunkasa harkar shari’a, ta zama babu sani babu sabo, duk wanda aka kama da laifi a hukunta shi. Idan haka ta kasance, dinbin dukiyar da Allah Ya ba kasar nan za ta zama mai amfani ga daukacin al’umma.
Lallai ne al’ummar kasa mu hadu mu yi karatun-ta-natsu, mu kasance masu canja halaye. Mu sanya kishin kasa da kishin al’umma a ranmu. Mu kasance masu bin doka da oda. Mu kasance masu son gina kasa. Mu tashi tsaye wajen neman na kai, mu guji zaman kashe wando da roko da tumasanci. Ta haka ne za mu taimaka wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran mukarraban da muka zaba, domin su gudanar da shugabanci mai kyau da inganci, wanda zai kawo mana arziki mai kima, ya wanzar mana da zaman lafiya da kwanciyar hankali da walwala. Haka kuma mu kasance masu yin addu’a, domin Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya, Ya magance mana duk wani mai neman kawo mana nakasu.
Ni Gizago da sauran al’umar kasa, muna taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shi da gwamnoni da dukkan masu rike da madafun iko addu’ar Allah Ya taya su riko, Ya ba su karfin niyya da ikon gudanar da mulkin adalci. Amin!