A yi adalci a binciken mutuwar dan kwallon Nijerirya a Uganda —Gwamnatin Sakkwato
Gwamnatin Sakkwato ta nemi a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda

Marigayi Abubakar Lawal. (Hoto: @viperssc).
Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda.
Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a lokacin da suke karbar gawar margayin a Nijeriya domin jana’izarsa a mahaifarsa sa ke jihar.
Injiniya Kofar Marke ya bayyana baƙin ciki da rashin Abubakar Lawal, wanda ya bayyana a matsayin ɗan kwallon ƙafa na musamman kuma jakada nagari a harkar wasanni.
“Labarin rasuwar nan abar girgiza da taba zuciya ce, domin marigayin ya bayar da gudunmuwa a harkaar ƙwallon ƙafa ta a-zo-a-gani a duniya ta hanyar ƙasashe daban-daban.
“Muna gode wa ofishin jekadancinmu da ya tabbatar da dawowar gawar margayin zuwa gida don yi mata janaza, haka ma makusantan abokansa suma sun yi kokari.”
Injiniya Mustafa ya ƙara tabbatar da goyon bayansu ga iyalan marigayin kamar yadda suka yi tsaye tun sa’adda lamarin ya faru har aka karbi gawar, bisa ga sahalewar gwamnan Sakkwato Ahmad Aliyu.
Dan kwallon Nijeriya Abdullahi Shehu ne ya rako gawar zuwa Nijeriya ya mika ta’aziyarsa ga iyalai da dangin margayin da mutanen Sakkwato da masoya kwallon kafa gaba daya.
“Abubakar Lawal ba kawai abokin hulɗa ba ne, aboki ne a gare ni, yana da karimci da sanin yakamata, ina rokon Allah Ya gafarta masa”.
Margayin ɗan kwallon Nijeriya ne da ya fara buga wasa a Sakkwato da Nasarawa kafin likafa ta ci gaba ya koma kasar Uganda, ya samu nasarori da dama a wasan ƙwallon kafa a lokacin rayuwarsa.