A yi addu’o’i kan halin da Nijeriya take ciki — MURIC

MURIC ta bukaci limamai da su jagoranci mabiya a masallatansu a gobe Juma’a.

A yi addu’o’i kan halin da Nijeriya take ciki — MURIC

Shugaban MURIC Farfesa Ishaq Akintola

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi ta Nijeriya (MURIC) ta buƙaci a gudanar da addu’o’i a masallatai da coci-coci a ƙasar kan abubuwan da ta kira da munanan alamu a harkokin siyasar ƙasar.

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya gabatar da buƙatar a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis.

MURIC ta nuna cewa gudanar adduo’i a masallatai da majami’u bukata ce da ta zama dole bisa la’akari da yadda baƙin al’amuran ke neman zama barazana ga makomar kasar baki ɗaya.

Saboda haka MURIC ta yi kira ga dukkan limaman Musulmi da su jagoranci mabiya a masallatansu a gobe Juma’a 9 ga watan Agusta, su yi addu’o’in, kamar yadda su ma limaman Kiristoci, su jagoranci mabiyansu wajen yin addu’ar a ranar Lahadi mai zuwa, 11 ga Agustan.

Farfesa Akintola ya ce waɗannan abubuwa na tashin hankali da suka lullube matasa a duniya, munanan alamomi ne da suke matuƙar buƙatar yi wa Najeriya addu’o’i.

Shugaban ya kuma ce su ma masu mulki akwai buƙatar yi musu addu’a ta samun kariya da kuma sanya tausayin talakawa wajen gudanar da mulkinsu.

MURIC ta yi kiran ne sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa ta lumana da ta rikiɗe ta zama tarzoma ta kashe-kashe da lalata dukiyar al’umma wanda ta ce, ƙasar na cikin mawuyacin hali.

Baya ga wahalhalun da ke tattare da durƙushewar tattalin arziƙi, zanga-zangar matsin rayuwa na ci gaba da fito da wasu al’amura marasa daɗi, ga ƙasar in ji ƙungiyar ta MURIC.

Sanarwar ta kara da cewa hatta masu shirya zanga-zangar ba su yi tsammanin irin wannan mummunan lamari zai faru ba.

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja

Solskjaer ya zama sabon kocin Besiktas

Nijeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar BRICS