A yi dukkan mai yiwuwa don zaman lafiyar kasar nan

Ina sake yi wa masu karatu da sauran al`ummar Musulmin duniya baki daya  Barka da Sallah, da fatan a daidai wannan rana da mai karatu yake karanta wannan makala Maniyatan kasar nan sama da dubu 70, da Allah Ya nufe su da zama cikin al`ummar Musulmin duniya sama da miliyan 2, da suka sauke farali […]

A yi dukkan mai yiwuwa don zaman lafiyar kasar nan

Ina sake yi wa masu karatu da sauran al`ummar Musulmin duniya baki daya  Barka da Sallah, da fatan a daidai wannan rana da mai karatu yake karanta wannan makala Maniyatan kasar nan sama da dubu 70, da Allah Ya nufe su da zama cikin al`ummar Musulmin duniya sama da miliyan 2, da suka sauke farali a bana, sun fara dawo wa garuruwansu, Ya sa kuma ibadar da suka gabatar makabuliya ce amin summa amin. Kasancewar a jiya Alhamis Hukumar kula da Aikin Hajji ta kasa wato NAHCON, ta shardanta ta zama ranar farko da za ta fara jigilar dawo da Maniyatan kasar nan, ta ce kuma da Maniyatan Jihar Gwambe za ta fara.

Aikin Hajjin bana nan dai daga kasar nan, shi ne wanda ya fi kowane aikin Hajji tsada a tarihin zuwa aikin Hajji ga maniyatan kasar nan tun ana tafiya da kafa, har ya dawo ta mota, zuwa ta jirgin sama da ake amfani da shi yanzu. A bana kowane maniyaci ya biya sama da Naira miliyan daya da rabi. Tsadar da Hukumar NAHCON ta ce ta samo asali ne daga irin yadda musayar Naira zuwa Dalar Amurka ta fi ta kowace shekara haurewa a kan farashi, bisa ga tabarbarewar darajar Nairar. Har hukumar ta NAHCON, ta ke ba da kariyar cewa a bara an ba Maniyatan canji a kan N197, kan kowace Dalar Amurka, sabanin a bana da darajar Nairar ta tabarbare ta koma a kan N305, kowace Dalar Amurka.

Amma kuma Hukumar ta NAHCON, ba ta ce uffan ba a kan kin bin shawarwarin da masu Kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama da harkokin yawon bude ido da suke jigilar Maniyata `yan jirgin yawo da daidaikun jama`a, kai har ma da wannan fili, na lallai akwai bukatar ta duba yiwuwar rage kudade irin na jiragen sama da na masaukai da na abinci da makamantansu, da niyyar sama wa maniyatan sauki.

Na bar irin yadda aka gudanar da aikin Hajjin, sai nan gaba in Allah Ya nufa. Yanzu bari in waiwayi yadda jama`ar kasar nan suka yi Salla babbar, bisa ga irin ibadar layya da masu halin yi suka gabatar a kan wannan babbar sunnah ta addinin Islama da ta dauko asali daga Annabi Ibrahin (AS). Tabbas dabbobi layya sun yi dan karen tsada a bana, musamman kananan dabbobi irinsu rago da tunkiya, akuya da bunsuru, wadanda su sunnah Manzo (SAW), ya fi jaddadawa a yanka, kuma su masu kananan karfi suka fi sukunin su yanka. Masu sana`ar saye da sayar da dabbobi sun jingina tsadar kananan dabbobin fiye da shanu ko rakumma, bisa ga wai irin tsadar da abincin dabbobin ya yi da kuma faduwar darajar Nairarmu. 

Masu hada-hadar dabbobin sun ce, hakan ta sa mutanen kasashen makwabtanmu irinsu Nijar da Kamaru da Chadi da a baya muke sayo dabbobi daga wajensu, suka rinka shigowa kasar nan, suna sayen dabbobinmu. Tsadar Dala ke nan da mai tuyar kosai ko dan wake na kasar nan da a kullum suke kafa hujja da ita, cikin kara matse hannu.

Rahotanni daga sassa daban na kasar nan, kai har ma daga kasar Saudiyya, sun yi nuni da cewa a bana ba a samu yawan mace-mace ko hadurra ba a cikin bukukuwan Sallar ko a aikin Hajjin na bana ba, don kuwa, zuwa kammala aikin Hajjin, maniyatan kasar nan da suka rasu ba su kai goma ba, kamar yadda shugaban ayarin ma`aikatan kiwon lafiya na kasar nan a aikin Hajjin Dokta Ibrahim Kana ya sanar. A nan cikin gida ma Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, ita ma ba ta bayyana lokacin shagulgulan Sallah Babbar ba a zaman an samu wasu hadurran da suka zarce hankali ba.

Sai dai kash! fadan da aka yi a Kano ranar Asabar kashegarin sallah, a lokacin hawan Daushe na mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na II, fadan da ake zargin ya faru ne tsakanin `yan Kwankwasiyya da Gadujiyya, wato mabiya tsohon gwamna kuma Sanatan Kano ta tsakiya Sanata Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso da na gwamna mai ci yanzu Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ko kusa bai dace ba, kuma abin da duk wani mai son zaman lafiya, kwanciyar hankali, kaunar juna da karuwar arzikin kasar nan da Jihar Kano baki daya, ya kamata ya yi tir da Allah wadai da shi. Don kuwa yanzu babban abin da ake begen gani a Jihar Kano, bisa ga matsayin da Allah Ya yi mata na cibiyar saye da sayarwar kasa nan da kuma irin mutanen kasar nan daban-daban da ma na kasashen waje da ta kunsa, to kuwa ba abin da Kanon take bukata da ya wuce wadancan abubuwa da na ambata a sama, wato zaman lafiya.  

Kodayake, jami`an tsaro a jihar da shaidun gano da ido, sun tabbatar da cewa ba ran da ya salwanta a wancan fada, amma an ji tsohon Kwamishinan Albarkatun Ruwa na gwamnatin Sanata Kwankwaso Dokta Inusa Adamu dangwani, yana fada wa tashar gidan Radiyon Freedom, cewa kimanin mabiyansu 20,  aka jikkata.Tashar Radiyon ta kuma ruwaito Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kanon Malam Mohammed Garba yana zargin `yan Kwankwasiyya da cewa su suka yiwo hayar `yan ta`addar daga jihohin da ke makwabtaka da Kano irin su Jigawa da Katsina da Zamfara da suka hada da na su na Kanon, su kuma kawo su don su wargaza hawan Daushen.

Kome ke hamzari ko neman biyan bukatar wadanda suka haddasa rikicin na Kano, ko kusa babu hankali, ba kuma manufa a yin hakan. Ba don komai ba na fadi haka ba, sai don irin yadda na ga sakonnin Barka da Sallar da shugabanni masu rike da madafun iko na wannan zamanin tun daga kan shugaban kasa da Sarakunan gargajiya da hudubobin Limaman idi bayan Sallar Idi da sauran shugabannin da har yanzu suke tofa ta albarkacin bakunnansu a kan harkokin yau da kullum na kasar da shugabannin kungiyoyin al`umma, duk sun maida hankali ne a kan `yan kasa a duk inda suke su zauna lafiya da junansu, tare da kauce wa duk wani abu da zai kawo tashin-tashina da gaba da kiyayya.

Ko shakka babu wadancan sakonnin da shugabannin suka aika ga mabiyansu a lokacin bukuwan Sallar, ba sa rasa nasaba da irin tashin-tashinar sai a sake fasalin zamantakewar kasar nan, da nemam tabbatar da kasar Biyafara da su matashi Nnamdi Kanu shugaban kungiyar neman tabbatar da kasar ta Biafara, wato IPOB da barazanar wa`adin 1 ga watan goben da gamayyar kungiyoyin matasan Arewa suka bai wa `yan kabilar Ibo mazauna Arewacin kasar nan da su kwashe yanasu-yanasu su bar Arewa kafin waccan rana.

Duk kuwa da irin tabbacin da aka samu na matasan sun janye wa`adin bayan sa-bakin Gwamnan Jihar Borno Alhaji Kassim Shettima, har yanzu shugabannin `yan kabilar Ibon, musamman mazauna Arewa da ma na can shiyyarsu ta asali shiyyar Kudu maso Gabas, hankulansu ba su kwanta ba.

Tabbas Salla babbar ta bana ta zo da tsadar rayuwa da rudanin rashin sanin makomar kasar nan da wasu shakkiyai suke kara rurutawa don son zuciyarsu. Wannan fili yana maraba da umurnin da shugaban kasa ya ba dakarun kasar nan da su yi dukkan mai yiwuwa wajen murkushe duk wani ko wasu da suke neman wargaza zamantakewar kasar