A yi hattara da mayaudaran ’yan siyasa
Editan Aminiya mai farin jini. Assalamu alaikum. ku ba ni dama in yi kira ga ’yan uwana matasa, wadanda ake amfani da su a matsayin karnukan farauta, domin biyan bukatan ’yan siyasa, wadanda ba sa ganin kimar mu sai lokutan zabe. Lokaci ya yi da za mu yi amfani da tunaninmu, mu daina amincewa ana […]
Editan Aminiya mai farin jini. Assalamu alaikum. ku ba ni dama in yi kira ga ’yan uwana matasa, wadanda ake amfani da su a matsayin karnukan farauta, domin biyan bukatan ’yan siyasa, wadanda ba sa ganin kimar mu sai lokutan zabe. Lokaci ya yi da za mu yi amfani da tunaninmu, mu daina amincewa ana amfani da mu, ana sanya mu tada husuma a loklacin yakin neman zabe. Mu sani cewa duk wanda zai zo ya raba gishiri ko shinkafa domin a kada masa kuri’a, to ku karbi kudin, tare da mudun shinkafan, domin rabon kune, amma kada ku zabe shi. Allah yasa ayi zabe lafiya amin. Daga Garba Nakwalo Ajaura Jihar Jigawa 08091927222.
Ta’aziyyar mutanen Potiskum
Salam Edita. Don Allah ka ba ni dama in jajanta wa al’ummar garin Potiskum da ke Jihar Yobe, bisa ga hare -haren kunar bakin wake da aka kai akan jami’an tsaron da fararen hula. Allah Ya jikansu da rahama, Ya kuma kare gaba amin. Daga Garba Sabiyola Sa ‘idawa Gashu’a.
Muna neman sauyi mai alfanu
Da ma sakaci da cin hanci da rashawa da rashin bin doka da oda da rashin iya mulki shi ya sa Gwamnatin Najeriya ba za ta iya jure faduwar farashin Man fetur ba a Najeriya. Yau abin kunya a nan, shi ne Shekara biyu ke nan shugaba Goodluck ya kasa zuwa zauren majalisa, wurin bayyana kasafin kudin Najeriya. Da fatan Allah ya yi mana zabi da gwamnati mafi alkhairin wnanan. Amin Daga Zaidu Bala kofa Sabuwa Birnin Kebbi, Jihar Kebbin Najeriya 07037697009.
Ga ’yan Najeriya
A gaskiya ya kamata ’yan Najeriya mu jajirce mu zabi Janar Muhammadu Buhari, a matsayin Shugaban kasa, a zaben 2015. Daga 07046107640.
Ga Editan Aminiya
Editan Aminiya sai fatan alkhairi a gare ku, duk da cewa da kukan yi aikin ajizanci, wanda ga sako ko makala mai muhimmanci, amma sai ku kawar da kai. To ni ban da damuwa in an saka abu mai ma’ana, an bar wanda ba shi da ma’ana, ko da kuwa nawa ne. A matsayina na dan Katsina, korafina zai iya zuwa tushen jaridar. Shawarata don Allah a dai kara kulawa da duk abokin hulda. Domin ai ku abokan tafiya ne, kuma muna alfahari da ku, duk da wannan sabanin fahimtar. Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519.
A yi zabe lafiya
‘Fata nagari Lamiri.’ Ba komai ba ne ya sa na fara da wadannan kalamai ba, mu dai addu’ar mu na zuwan Kofi Annan Najeriya, ita ce akan tattaunawarsu da hukumomin zabe don samun ingantattun zabuka da kwanciyar hankali a kasa Allah Ya sa kwalliya ta biya kudin sabulu, ba ya tafi ya bar baya da hatsaniya ba. Hakika mu dai al’ummar Najeriya, muna bukatar canji. domin a kullum muna cikin zullmi da rudani. Allah Ya sa a yi zabe lafiya, a kare lafiya. Daga Alhaji Umar Foreber Gashua 08108003333.
PDP ta yi rauni a Kebbi
Edita siyasar Jihar Kebbi ta dauki wani sabon salo, inda masu rike da mukami ke ajiyewa, suna komawa Jam’iyyar adawa ta APC, ganin irin yadda son kai ya mamaye Shugabancin Gwamnnatin Kebbi, har zuwa yau da shi ke ganin kamar yana iya fitar da kitse wuta, inda ya hana a tsaya a yi zaben fitar da dan takarar gwamna a PDP. Jam’iyyar PDP ta yi rauni a Kebbi. Allah Ya kawo mana sauyi mai amfani. Amin. Daga Usman Adamu Aliero, Jihar Kebbi. 07061594299.
Mu bi Allah
“Kome ya yi zafi maganinsa Allah“. Na fara da wannan dangane da cigaba da kai hare-haren ta‘addanci da ‘yan a ke yi a yankin Arewa maso Gabas, musamman a jihohin Borno, Yobe da Adamawa. Rayukan bayin-Allan da ba su ji ba, ba su gani ba sun salwanta. Hakika komawa ga: Allah tare da kaurace wa ayyukan sabo, gami da kyautata mu‘amala tsakaninmu, ita ce hanya kadai da za ta kawo mana karshen wannan bala‘i. Allah ka yi mana maganin duk wata kungiya da ke amfani da sunan Musulunci wajen tayar wa al’umma hankali. Daga Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382.
Kira ga ’yan Najeriya
Edita zan yi kira ga al’ummar Najeriya kan lallai mu yi kokari na zahiri, kuma badini mu bar wa Allah ta hanyar addu’ar, don kawo karshen musifun da ke damun kasar nan. Allah Ya ba mu shugabanni nagari. Allah Ya maido wa yankin Arewa maso gabas zaman lafiya. Daga Ummu Adiya Gusau, Jihar Zamfara 08147952262.
Neman tsari daga bala’i
Aminiya ki gaya wa kasar Faransa, cewa muna addu’a kan bala’i da musifar jarrabawa, irin namu ya afka musu. To, Allah Ya kawo mana sauki,. Daga Yusuf Abuja 07041403612.
Addu’a ga kasa
Masu neman tarwatsa kasar nan, masu mulki ne ko talakawa, Allah Ya yi manba maganinsu. Domin akwai ranar kin dillanci. Daga Gambo Kassim Garun Ali, Garko, Jihar Kano 08060001330.
Ga ’yan Jigawa
Lamido ya shafa mana kashin kaji, inda ya jawo, mu mazauna Legas an ace mana ’yan kauye ne. Katsinawa da ’yan Bauchi na yi mana gori. Lamido mu dai ba mu yafe ba. Saboda haka sai mu yi zaben da zai kawo mana sauki. Allah ya yi mana zabi nagari. Daga Yahaya Ahmad Jabo, Apapa Legas 08026392800.
Ga Malam Elzazzaky
Edita don Allah ka mika min gaisuwata ga Malam Ibrahim Elzazzaky, zariya. Allah Ya kara wa Mallam lafiya da juriya. Sannan ina son bai wa malam shawara kan ya yi hakuri da mhassada, masu son wnai rikici ya taso daga wurin dalibanka. Don Allah ka kar ayin hakuri, ka bar su da Allah. Daga M.K. Ibrahim Apapa, Legas 08182839818.
Ga alkalai
Alkalai a ji tsoron Allah. In har suka yi shari’a ta adalci, sun tsira. Domin akwai takaici kan yadda ake gudanar da shari’a a kasar nan, misalin gwanjon shanu a Jihar Neja da kuma Kwasau da ta kwashe kudin marayu, ’ya’yan Alhaji Yahaya Round. Gwamnati a bi kadin hakkin bayin Allah da ake tauyewa a kusan kullum. Allah Ya kawo mana dauki. Daga Muhammad Gumel 07058835510.
Ga Gwmana Shema
Edita don Allah ba ni fili in yi godiya da addu’a ga Shema mai albarka, kan yadda ya rike mu, cikin adalci da tausayi. Allah Ka yi masa zabi mafi alkhairi a rayuwa. Daga Amiru Isa Bakori 080759599086.
Ga samarin Arewa
Gaisuwa da jinjina a gare ku. Aminaina, ina so ku ba ni dama in yi kira ga samari cewa ya ku samarin Arewa abin alfahari ne, abin so ne, kuma kashin bayan kowace al’umma. Sai dai me ya smaeku ku ke aikata sata da fyade da fashi da sauransu. Kuna tunanin cewa za a ci gaba da sonku da tutiya da ku a haka? Daga (Maman Abba), A’isha Zariya. 08033272211.