A yi koyi da Malam Isiyaku Dikko wajen yi wa al’umma hidima
Sanya wanda ya cancanta ya kula da wuri shi ne nasarar kowane shugaba. Irin nasarar da Hukumar Kare Muradun karni ta samu a Jihar Katsina, karkashin jagorancin Malam Isiyaku Dikko, wanda yake masanin ilmin siyasa ne, malamin makaranta, manazarci, marubuci kuma dan jarida; wani abin nazari ne da misali ga wadanda suke neman ci gaban […]
Sanya wanda ya cancanta ya kula da wuri shi ne nasarar kowane shugaba. Irin nasarar da Hukumar Kare Muradun karni ta samu a Jihar Katsina, karkashin jagorancin Malam Isiyaku Dikko, wanda yake masanin ilmin siyasa ne, malamin makaranta, manazarci, marubuci kuma dan jarida; wani abin nazari ne da misali ga wadanda suke neman ci gaban al’umma da kasa baki daya.
Majalisar dinki Duniya ta kafa MDG da tallafin duk kasashen da wannan hukuma za ta yi wa aiki da kuma wani kaso, wanda duk jihar da za ta yi aikin za ta bayar. An kafa ta bisa manufofin karfafa ilmin firamare ingantacce, yaki da fatara da talauci da kuma hadarin kamuwa da yunwa a kasa, rage matuwar kananan yara a wajen haihuwa, inganta samun kula da lafiya ga masu juna biyu, yaki da cutar maleriya, kanjamau da sauran cututtuka masu saurin yaduwa a cikin al’umma.
Wani tsarin bayyana ayyukan hukumar a Katsina, kamar yadda Malam Isiyaku Dikko yake yi lokaci-lokaci, shi ne buga littafi na zallar hotunan ayyuka da cikakken adireshin inda aka gudanar su. Idan mutum zai samu littattafan da hukumar ta Katsina ta buga, na hotunan wadannan ayyukan sai ya yi tsammanin ayyukan Gwamnatin Tarayya ne.
A wasu jihohin, ofishin hukumar MDGS wata matattarar ’yan siyasa ce kuma ba a ba kowa sai dan-ga-ni-kashe-nin-siyasa, wanda hakan kan dakile aikin da ya kamata a yi, sai dai harkar siyasa.
A tsarinsa, kowane zangon aiki, bayan kammala shi, a yi littafi, wanda ke dauke da hotunan inda aka yi aikin, garin, unguwa da inda aikin yake. An yi wadannan littattafai da Hausa da kuma Turanci. Idan ka samu littafin, ba ka bukatar tambayar ina aka yi aiki kaza? Kuma kana isa wajen za ka ga allo a rubuce na aikin da aka yi. Ya fi amincewa da tsarin gani da ido maganin tambaya.
A Katsina, ofishin MDGS ofis ne na yin aikin da aka tsara zai aiwatar. Akan haka daga kafa ta Katsina zuwa yau, sun gina rijiyoyin burtsatse masu yawan gaske. Sun gina famfunan tuka-tuka sama da dubu daya. An gina dakunan haihuwa da na ganin likita da dama. An gina dakunan bahaya masu armashi.
An horar da masu cutar yoyon fitsari, an yi ayyuka daban-daban na yaki da cututtuka masu yaduwa, irinsu maleriya, cutar fuka da sauransu. A Yanzu haka hukumar na wani gagarumin shiri na tallafa wa masu sana’ar noman rani, masu sana’ar fawa da kuma mata masu sana’ar dinki.
A tsarin hukumar ta Katsina, duk aikin da aka ba ka, dole ka yi ingantattace kuma mai aminci, dole ka yi amfani da kaya wadanda aka tabbatar karbabbu ne. Duk wani dan kwangila a Jihar Katsina yana shakkar aiki da hukumar, don ya san Malam Isiyaku bai yadda da aikin sama-sama ba.
Da kansa yakan fita, ya je wajen aikin ya tabbatar da an yi kamar yadda yake a takardar da aka ba ka aikin, sannan ya sanya hannu a biya ka kuma hukumar ta fi kowane wajen sauki da saurin biyan dan kwangila. In ka tabbatar ka yi aikinka yadda ya dace, to ka koma gidanka ka zauna za ka ji kira.
Wannan ya sa duk kwamitocin da akan kafa don su bi jihohi suna duba ayyukan da MDGS kan yi, suka ba ta Jihar Katsina na daya sannan sauran suka biyo baya. Sukan kuma nuna jinjinarsu ga hukumar duk inda suka je. Sanata Kanti Bello, lokacin da yana Majalisa Tarayya, ya sha takama da jinjina ayyukan hukumar ta Katsina. Kwanan nan da kwamitin Majalisar Wakilar ta zo Katsina, a ziyarar jihohin da ayyukan MDGS suke, Alhaji Gambo danmusawa, dan jam’iyyar CPC da ke wakilatar kananan hukumonin danmusa, ya jinjina wa ayyukan, ya ce duk jihar da suka je ba wadda ta yi kusa da Katsina.
A Wasu jihohin, ofis din MDGS za ka gane shi ko daga nesa saboda manyan alluna za su yi maka maraba. A Katsina ba wannan, za ka ga tambarin hukumar ne kawai a ayyukan da ta yi. Ko shiga cikinsa ka yi, ba wani wuri da za ka ga wata alama na cewa wannan ofis na hukumar ne. Alama kawai ita ce aiki ba dare ba rana, ba kuma Asabar ko Lahadi. Duk lokacin da aiki ya kama, haduwa za a yi a aiwatar da shi.
A Katsina, ilahirin ma’aikatan hukumar ba su kai goma ba, don haka kowa ka iske yana cikin aiki, a duk lokacin da ka same shi. Su ma aro su aka yi daga wasu ma’aikatun. Tsarin Isiyaku Dikko shi ne, kowane aiki a yi tanda, wanda ya ci a ba shi aiki, ya tafi wajen aikinsa.
Malam Isiyaku Dikko mutum ne mai bin ka’ida. Duk abin da aka sa a gaba, to in an bi ka’ida shi ke nan bai da ja. Wannan yasa ake fassara shi da mai wahalar sha’ani kuma ake tsoron matsawa kusa da shi. Ko me zai hada ku, yana son ka gamsar da shi da hujja. Bai yarda da shiga harkar kowa ba. Bai kuma sha’awar ka shigo ta shi, in bai sanyo ka ciki ba.
danjuma dan jarida ne da ke zaune a Katsina, 08035904408, [email protected]