A yi magana kafin kurewar lokaci
Tsohon Gwmamnan Jihar Anambara, Dokta Chukwuemeka Ezeife, ba dadadewa ba, ya bayyana cewa mugun aiki da keta dokar masu fafutikar kafa “Biafra” sun auku ne saboda take-taken Shugaba Muhammadu Buhari sun tursasa mutanen yankin Kudu maso Gabas har suka fara tunanin ballewa daga Najeriya. Wannan bayani za a dade da ana tuna shi a matsayin […]
Tsohon Gwmamnan Jihar Anambara, Dokta Chukwuemeka Ezeife, ba dadadewa ba, ya bayyana cewa mugun aiki da keta dokar masu fafutikar kafa “Biafra” sun auku ne saboda take-taken Shugaba Muhammadu Buhari sun tursasa mutanen yankin Kudu maso Gabas har suka fara tunanin ballewa daga Najeriya. Wannan bayani za a dade da ana tuna shi a matsayin wautar da wani babban mutumn mai nisan shekaru ya taba yi a Najeriya. Ezeife ko daya daga cikin masu fafutikar da zai iya bayar da kwakkwarar hujja cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya aikata don cutar da hakkin ’yan kabilar Ibo, tun daga watan Mayu ko kuma wani sashe na kasar nan, da zai bayar da kafar yin barazanar ballewa. Ire-iren su Ezeife ke kirkiro kkiren karyar laifuka da suke alakantawa da “take-taken.”
Duk da munanan kalaman Ezeife, hakikanin gaskiyar lamari wannan fafutikar kafa kasar Biyafura tun kafin kafuwar Gwamnatin Buhari take na tsawon shekaru. Wannan mummunan kuduri ne da miyagunj mutane masu tsananin son rai ke amfani da shi, wajen zuzuta al’amura don jefa kasar nan cikin rikici. kungiyar fafutikar kafa kasar Biyafura ta MOSSOB, an kafa ta ne tsawon shekaru kafin Buihari ya zama shugaban kasa. Haka kuma, “rediyon Biyafura,” da aka kafa bisa keta doka da mummunar manufar boye yana yada kalaman cusa kiyayya da gaba gha sauran ’yan Najeriya tun ma a zamanin mulkin Jonathan, wanda ya kamata a ce ’yan kabilar Ibo sun amince da shi a siyasance. Yamutsin kwananan ya auku ne a kan irin makircin Nnamdi Kanu ya kulla na zuzuta na “Mutanen asalin kasar Biyafura,” wadanda bayan sun balle daga kungiyar MOSSOB suka kafa gidan rediyo da suke amfani da shi wajen yada akonnin gaba da kiyayya.
Gaskiya ne yankin Kudu maso Gabas da ke kasar Ibo na fama da matsalolin da dama da suka hada da na muhalli da tattalin arziki da na zamantakewa, amma ai saauran sassan kasar nan na fama da makamantan matsaloilin. Wakilansu a gwamnati sun nuna gazawa wajen ganin an cusa ayyukan raya kasa na yankunan a cikin kasafin kudi, su kuma tabbatar an aiwatar da su. Baya ga Majalisar Tuntuba ta Gabashin Najeriya, da ya dora wa Kanar Ojukwu kafa Jamhuriyar Biyafura a shekarar 1967, babu wata kafa ko dandamalin kabilar Ibo da ya amince wa wani mutum ko kungiyar mutane su yi fafutikar kafa Biyafura. Kafin rasuwarsa, gwarzon yakin Biyafura, Cif Odumegwu Ojukwu, Ikemba na Nnewi ya yi takarar shugabancin Najeriya sau biyu, a tsakanin shekarun 2003 da 2007, a karkashin tutar jam’iyyar APGA. Ya bayyana kararaa wancan lokacin, cewa, bukatun hkkokin kabilar Ibo za a iya cin musu ne kawai a dunkulalliyar Najeria.
Sai dai kuma wani al’amari na saba wa hikimar Ikemba, it ace, ta bangaren Mista Uchenna Madu da ya balle a matsayin shugaban MOSSOB ya furta cewa, an tauye ’yan kabilar Ibo, ana nuna musu danniya, inda aka yasar da su. Wannan kururuwa bat a da tushe. Da kabilar Ibo ake damawa a kundin tsarin mulkin Najeriya, tun daga shekarar 1978, kuma sun samu wakilci a gwamnatance tun daga wancan lokacin, har ma mataimakin shugaban kasa da shugaban majalisar dattijai da shugaban majalisar wakilai suka yi, tare da shugaban kotun koli da ministoci da sakataren gwamnatin tarayya da shugaban rundunar sojoji da shugaban rundunar sojan ruwa da shugaban sojan sama da sufeto-janar na ’yan sanda.
kungiyoyin kabilun yankin Kudu maso Kudu sun cire kansu daga wannan kasar “Biyafura,” da aka yi azarbabin zana taswirarta, ake yadata karara a yankin Gabas.l shugabannin kabilun Itsekiri da Ijaw da Urhobo sun yi tur da jefa su cikin yunkurin kafa Biyafura, inda suka tabbatar da mubaya’arsu ga Najeriya guda. A gaskiya lamarin na da daure kai wajen fahimtar hikimar masu zanga-zanga. A lokacin da suke ikrarin cewa, suna fafutikar ganin an sako shugabansu, gaskiyar da ke da saukin fahimta, ita ce, kotu ta bayar da belin Kanu, amma babu daya daga cikin magoya bayansa da ya yi kokarin cika sharuddan belin. Sabanin taimaka masa ya cika sharuddan belin, sai ma tara kudi da suke yi don daukar nauyin gudanar da zanga-zangar ganin an sake shi.
Mista Nnamdi Kanu ya yi wauta da mummunar barazanar “kashe kowa a Najeriya idan aka hana mu kasar Biyafura,” ga shiu kuma ya shiga hannu, don haka zai amsa tuhumar ta’addancinsa da cin amanar kasa. Mummunar tarzomar titi da ya sanya miyagun matasa ba za su ba shi kariya a kotu ba. Saboda haka, muna kira ga shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya da ke yankin Kudu maso Gabas su ja kunnen wadannan matasa marasa tarbiyya su dawo bisa turba, kafin al’amura su wuce kima. Kamata ya yi gwamnonin Kudu maso Gabas da kungiyar Ohanaeze Ndi’igbo su yui Magana tun yanzu don kashe wutar da ke ruruwa.