A yi nazari dai Aminu Waziri Tambuwal
Sunan Aminu Waziri Tambuwal ba boyayye ba ne ga daukacin al’ummar Najeriya. Mukaminsa na Shugaban Majalisar Wakilai ta kasa sananne ne kusan ga kowa. Yanayin gudanar da aikinsa (kwarewa da kuma rashinta, dai-dansa da kuskurensa) a bayyane suke tamkar hasken rana ga masu sharhi akan al’amuran yau da kullum. Saboda wannan ne ma ya sa, […]
Sunan Aminu Waziri Tambuwal ba boyayye ba ne ga daukacin al’ummar Najeriya. Mukaminsa na Shugaban Majalisar Wakilai ta kasa sananne ne kusan ga kowa. Yanayin gudanar da aikinsa (kwarewa da kuma rashinta, dai-dansa da kuskurensa) a bayyane suke tamkar hasken rana ga masu sharhi akan al’amuran yau da kullum. Saboda wannan ne ma ya sa, nake ganin ni ma nan da ba kowa ba, zan iya gane rigimar da take daidai da shi, kamar yadda kai tsaye nake iya gane rigimar da ta fi karfinsa.
Kiran da wasu mutane ke yi wa Aminu Waziri din domin ya fito takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC tun bai riga ya bayar da sanarwar ficewarsa daga PDP ba, kira ne da zan iya siffanta masu yinsa da masu raunin tunani. Kuma duk wani mai yin wannan kira, ina mai tabbatar masa da cewa girmansa ya gama faduwa kasa war-was a idanuwana da kuma idanuwan sauran ma’abuta hankali da ke Najeriya da ma duniya baki daya. Saboda rashin kishinsa ga Najeriya da rashin tunaninsa mai zurfi ya fito fili karara.
Kafin muje da nisa, bari in fito fili in bayyana me nake nufi. Aminu Waziri Tambuwal ba zai iya rike shugabancin Najeriya a halin da take ciki yanzu! Wallahi ba zai iya ba.
Da za ka tambaye ni, da zan gaya maka cewa Aminu jarumi ne da muke bukatar irinsa a cikin harkokin gwamnati. Domin mutum ne tsayayye da jama’a suke yaba aikinsa da salon mulkinsa. To sai dai wannan ya tsaya ne kawai ga iya majalisar da yake jagoranta yanzu, da kuma wasu ‘yan ranke-ranken mukamai irin wancan. Amma zancen shugabancin kasar nan kam a halin da take ciki yanzu, to sama ta yi wa yaro nisa. Kuma idan ana zancen bindiga, bai dace a yi maganar wuka ba. Aminu Tambuwal Ya na iya kokarinsa, kuma muna yaba masa, har ma da addu’ar fatan hairi. Sai dai majalisa ba fadar shugaban kasar Najeriya ba ce! Tamkar matukin babur ne, da yake tunanin kamar zai iya tuka jirgin sama.
Babban abin da yake ban haushi da mahukunta a wannan kasar shi ne, ko da yaushe sai ka ga suna al’amura tamkar wasu dabbobin da ke rayuwa a cikin daji. Eh mana! In ba dabbar daji ba, wa zai kalli irin wannan hali da Najeriya take ciki, kuma har ya yi tunanin irin maigirma Aminu Waziri Tambuwal zai iya shugabantar ta? Wai kuma ana nufin masu wannan tunani ‘yan kishin Arewa ne, kuma kishin Arewar ne ya sanya su neman Tambuwal ya tsaya takara.
Bisa ga aiki na ma’abuta hankali, ai ko da ba su son Janar Muhammadu Buhari ne, ko kuma ba za su iya dafa masa ba saboda wasu maslahohi na kansu, ya kamata ne su yi nazarin wani mutum daban da zai iya yin wannan jan aikin.
Hukumomin Najeriya su fahimci cewa, an daina rudarmu da addini, kabilanci ko bangaranci. Abin da muke bukata shi ne mai kishin Najeriya ba mai kurin kishin Arewa ba. Duk wadanda suka halaka arewar ba ‘yan Arewa ba ne? Farkon musibar da ta fara tunkaro Arewa ba dan Arewa ne ya janyo ta ba? Allah Ya jikan marigayi Umar Musa ‘Yar’aduwa da gafararSa, amma ko ba ka da adalci ka san zamaninsa ne wannan musibar ta fara, kuma ita ce ke tafiya har yanzu tana neman wargaza kasar baki daya. Kuma gwamnatinsa ce ke da alhaki dari bisa dari akan al’amarin, saboda rashin iya jagoranci yadda ya dace na jam’iyar PDP.
A lokacin da Obasanjo ya dauko marigayin domin yin shugaban kasa, kungiyoyi da dama da ‘yan siyasa, malamai da ‘yan jarida sun yi ta ankarar da shi cewa wannan rigimar ba karama ba ce, kuma ba zai iya ta ba. Najeriya ba Jihar Katsina ba ce. Amma da aka yi rashin sa’a, sai ’yan zuga suka zuga shi, domin ganin bai ja baya ba, kamar yadda ‘yan zuga suke zuga Aminu Waziri yanzu.
Idan Allah zai sa Aminu Waziri ya tsaya ya yi nazari da kyau, zai fahimci me nake cewa. Wadanda suke zuga shi, suna yi ne kawai domin maslahar kansu ba maslahar al’umma ba. Ba wani guri da suke da shi wanda ya wuce a ce su ne silar zamowar wane akan mukami kaza. Wannan kuma saboda su samu damar yin yadda suka ga dama da dukiyar al’umma.
Ko shakka babu, duk wanda zai rike shugaban kasa a 2015, to lallai tilas ne, sai ya yi da gaske. In ba haka ba, bakin wutar zai karasa mutuwa a hannunsa, koda kuwa Janar Buharin ne! Kuma al’ummar Najeriya ba za su taba yafe wa wanda Najeriya ta karasa rugujewa a hannunsa ba.
Yanzu an zo wani lokaci da, ba wai ’yan kishin Arewa muke nema ba, ’yan kishin Najeriya baki daya ba tare da la’akari da kabila ko yanki ba. Da Aminu Waziri zai gane, da ya dawo gida ya yi wa addinin Allah hidima a cikin dukiyar da ya mallaka, ya amfana da sauran abinda ya rage na rayuwarsa. Saboda Allah Ya nufi gidansu gida ne na addini da kuma sarauta. Idan kuma bai fahimci haka ba, to ba wani abu da ya rage masa face shan wahala da ciwon zuciya. Ka dai yi nazari Aminu Waziri Tambuwal.
Nasir Abbas Babi 08033186727