‘A yi sulhu da Boko Haram’

Babban Editan jaridar Bauchi Lokaci Ya Yi, Malam Husaini Abubakar ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta yi sulhu da ’yan kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da tada kayar baya a jihohin Borno da Yobe da ke ci gaba da fuskantar hare-hare. Da yake zantawa da Aminiya a Bauchi Malam Husaini Abubakar ya ce zaman […]

‘A yi sulhu da Boko Haram’
‘A yi sulhu da Boko Haram’

Babban Editan jaridar Bauchi Lokaci Ya Yi, Malam Husaini Abubakar ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta yi sulhu da ’yan kungiyar Boko Haram da ke ci gaba da tada kayar baya a jihohin Borno da Yobe da ke ci gaba da fuskantar hare-hare. Da yake zantawa da Aminiya a Bauchi Malam Husaini Abubakar ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankali shi ne babban sinadarin da ke jawo ci gaban kowace kasa. Ya nuna damuwa bisa abubuwan da suke faruwa a jihohin Borno daYobe da Adamawa inda tashe-tashen hankula suke hallaka dimbin rayukar al’umma da lalata dukiya. A wani labarin kuma Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi Alhaji Abdulkadir Ibrahim Muhammed (Cikasoron)Bauchi ya shawarci matasan jihar su ci gaba da bada goyon bayansu ga gwamnatin Malam Isa Yuguda, saboda suna cikin wadanda suka fara amfana da ita tun shekarar 2007 zuwa yanzu. Shugaban Ma’aikatan ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa a lokacin da kungiyar Ci gaban Matasan Arewa (Arewa Youth Mobilization Forum) suka kai masa ziyara. Shugaban kungiyar Alhaji Abdullahi Musa Naira ya ce lokaci ya yi da al’umma za su cire hassada da son zuciya su rika fadin abubuwan alheri da gwamnatin Yuguda ta yi. Ya ce sabon filin jirgin saman Bauchi da sabon Asibitin kwararru da Gwamna Yuguda ya gina an kammala sama da kashi/95 cikin 100, don haka ya bukaci jama’a su ci gaba ba da goyon baya ga gwamnatin don samun nasarar bunkasa jihar.