A yi wa gwamnati uzuri kan hana shigo da shinkafa ta iyakokin kasa – Sarkin Kazaure
Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Husaini Adamu bukaci a yi wa gwamnati uzuri kan hana shigo da shinkafa ta iyakokin kasa, inda ya ce marasa gaskiya suna fakewa da shigowa da shinkafa ta iyakokin kasar nan suna shigowa da makaman da ake hallaka ’yan Najeriya. Alhaji Najib Hussaini Adamu ya bayyana haka ne a […]

Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Husaini Adamu bukaci a yi wa gwamnati uzuri kan hana shigo da shinkafa ta iyakokin kasa, inda ya ce marasa gaskiya suna fakewa da shigowa da shinkafa ta iyakokin kasar nan suna shigowa da makaman da ake hallaka ’yan Najeriya.
Alhaji Najib Hussaini Adamu ya bayyana haka ne a jawabinsa na ranar Sallar da ta gabata a fadarsa, inda ya shawarci jama’ar kasar nan su ci gaba da yin hakuri a kan kuncin rayuwar da suke ciki kan hana shigo da shinkafar ta iyakokin kasa, inda ya ce su yi wa Gwamnatin Tarayya uzuri kan hana shigo da shinkafar da ta yi ta kan iyakokin domin ta yi haka ne don tsaron rayukansu.
Alhaji Najib Hussaini Adamu ya ce matakin da gwamnatin ta dauka na hana shigowa da shinkafa ta iyakokin kasa, yana da ma’ana mai kyau domin an yi haka ne saboda wadansu batagari suna amfani da damar wajen yin ungulu da kan zabo suna zuba makamai a cikin buhunan shinkafa suna shigowa da su kasar nan wadanda da su ne aka amfani ake hallaka jama’a.
Sarkin ya nuna damuwa kan yadda jama’a suke yi wa lamarin hana shigo da shinkafar tab iyakokin kasa mummunar fassara, inda y ace da sun san hadarin da haka ke haifarwa ga Najeriya da ba su yi kuka da hakan ba, idan suka dubi irin halin da jama’a suka samu kansu a baya.
Alhaji Najib Hussain Adamu ya ce hatta man girki da ake amfani da shi a wancan lokaci ana shansa ne cikin hadari domin da dama daga cikin man girkin gurbattu ne wasu kuma sun riga sun lalalce saboda lokacinsu ya gama amma ana shigowa da su ana sayar wa jama’a.
Sai ya yaba wa jami’an tsaro kan kokarinsu wajen dawo da zaman lafiya a kasar nan musamman a nan Arewa inda ta’addancin ’yan Boko Haram ya fi kamari. Sarkin ya shawarci masu tayar da kayar bayan su rungumi zaman lafiya su zo a zauna a teburin sulhu, in kuma sun ki jama’a za su ci gaba da yi musu addu’a Allah Ya tarwatsa su.
Ya ce shekara uku baya a masarautarsa babu damar ya yi bikin hawan salla saboda tsoro da dar-dar da kasar nan take fama da shi, amma ga shi yanzu saboda daukar matakai a kan marasa gaskiya da yaki da ta’addanci ya sa an samu zaman lafiya.