A yi wa talaka adalci a Kano

Masu mulkin Kano damar talaka na hannunku, don haka kada a bari a cutar da al’umma da sunan ayyukan raya kasa. Na yi wannan matashiya ne, ganin himmar Gwamnatin Jihar Kano na fadada titunan Jiha, musamman a karamar Hukumar Fagge.Lallai Maigirma Gwamna da ’yan Majalisara Jiha, ya kamata kusan cewa akwai talakawan da suka sayi […]

A yi wa talaka adalci a Kano
A yi wa talaka adalci a Kano

Masu mulkin Kano damar talaka na hannunku, don haka kada a bari a cutar da al’umma da sunan ayyukan raya kasa. Na yi wannan matashiya ne, ganin himmar Gwamnatin Jihar Kano na fadada titunan Jiha, musamman a karamar Hukumar Fagge.
Lallai Maigirma Gwamna da ’yan Majalisara Jiha, ya kamata kusan cewa akwai talakawan da suka sayi gidaje, wadanda asalin masu gidajen sun ci kan iyaka, ko sun ketara filin da aka shata. Don haka koda an biya diyya a baya, ko ma ba a biya ba, wajibi ne a yi wa talaka adalci, domin abin da ya dade yak enema tun farkon kafuwar kasar nan.
Sannan ta hanyar hakan, Allah ya sanya damarTalakawa a hannunku, mazauninku namanyan wakilai a Gwamnati da kuka cancanta da jibantar lamuran talakawanku.
Da wannan ne, nake ganin ya kamataku yi duba zuwa koken da talakawan ku ke yi dangane da wannan aiki na hanyar wuji-wuji da gwamnatin jihar Kano ta fara yi.
Masugirma ‘yanMajalisa: Ku sani a yanzu talakawa suna cikin wahala ba kowa ke iya cin abinci sau uku a gidansa ba, saboda babu kudi a hannunjama’a.
Sannan ga dawainiyar rayuwa ta yau da kullum, bayan haka muhalli abu ne mai matukar muhimmanci ga kowane mutum, wanda ko haya ba ba ya  iya biya balle samun na ka gidan!
Don haka naga ya kamata ku duba girman Allah ku tuna ababen tambaya ne ku, bisa hakkokin talakawanku, lallai ya kamata ku tsaya kai-da-fata wajen kare martabar al’ummarku, ku tabbatar da cewa duk mutumin da aikin nan ya shafa gwamnati ta nema masa kyakkyawar makoma, kada ya wofinta.
Wannan mulki ne da talaka yake alfahari da shi, sabanin mulkin soja, don haka duk tsarin da zai kawar da talakawa dagacin moriyar aikin ya kamata a janyeshi.
Kamar shingen katanga tsakanin talakawan da titinmota, kamar yadda aka kafe a taswirar aikin. Sannan Gwamnati ta bayar da cikakkiyar dama ga talakawa, su ginasauran mitocin su da ba su shiga cikin awo ba, ko da hadi da irin tsarin da take so su yi ne.
Idan an yi haka talakawa za su kara fahimtar manufar wannan gwamnati ta ciyar da garin gaba da yada arziki a tsakaninal’ummarta.
Mun dai san Gwamnatin Kwankwaso ita ke horar da matasa sana’o’i; ita ta shirya auren zawarawa; ita ke fafutikar ganin ana bin dokokin hanya, don haka ta kafa Hukumar KAROTA. Matukar wannajn gwamnati na bukatar ganin turbar adalci da ta hau kai ya dore, wajibi ne ta kara himma wajen yi wa talakawa adalci. Laifin duk da ba na su ba, kada a kama su da shi, tunda Mahaliccinmu Allah (SWT) ya ce, “wani rai ba ya daukar zunubin wata.”
Daga karshe nake addu’a Allah ya ba ku karfin gwiwar yi  wa talakawanku daidai, su gane adalcinku. Amin.
Allah ya kawar mana da son zuciya da zalunci da ke zama silar tashin hankali a tsakanin al’umma. Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya a jihar mu, da ma kasa baki daya. Amin
Tukur Musa ya rubuto wannan wasika daga Fagge cikin birnin Kano.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno