A Zaben Gobe: Abubuwan da ya kamata mu kula da su

karshen tika-tika-tik! Masu iya magana dai sun ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya. Domin kuwa yau makonni shida da aka diba domin gudanar da zabe sun cika, idan Allah Ya kai mu gobe Asabar (28)3)2015), al’ummar Najeriya za su fita domin kada kuri’unsu, da nufin zaben Shugaban kasa da […]

A Zaben Gobe: Abubuwan da ya kamata mu kula da su
A Zaben Gobe: Abubuwan da ya kamata mu kula da su

karshen tika-tika-tik! Masu iya magana dai sun ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya. Domin kuwa yau makonni shida da aka diba domin gudanar da zabe sun cika, idan Allah Ya kai mu gobe Asabar (28)3)2015), al’ummar Najeriya za su fita domin kada kuri’unsu, da nufin zaben Shugaban kasa da Sanatoci da kuma ’Yan Majalisar Tarayya.

A yayin da al’umma ke zumudin fita kada kuri’a gobe, ni kuma ta fannina, ina da wasu shawarwari da nake son al’umma su yi la’akari da su. Wadannan shawarwari, babu shakka abin dubawa ne, muddin dai muna son haihuwar da mai ido ga kasarmu Najeriya.
Ya kai dan Najeriya, a yayin da ka kakkabe katinka na rijista, ya kamata ka tuna da cewa Najeriya tana cikin wani kangi, tana hannun garken kuraye, wadanda suka wawashe mata dukiya. karamin misali shi ne, yadda shugabanni suka mayar da satar dukiyar al’umma tamkar wani abin alfahari. Misali, mu duba yadda aka wawashe Dala bilyan ashirin daga asusun matatar mai ta kasa (NNPC), mu duba yadda aka sace makudan kudin ’yan fansho, mu duba yadda aka sace Dala bilyan tara, aka fitar da su a jirgin sama da nufin wai sayo makamai. Mu tuna da yadda a kullum ake sace danyen man fetur din kasar nan, wanda makudan kudi ne ake asara ta wannan hanya. Mu tuna cewa wannan kati da ke hannunmu zai iya kawo mana canji, musamman idan muka zabi mutumin da zai magance dukkan wadannan bahallatsa. Mu zabi jajirtacce, nagartacce, mai gaskiya, wanda ba zai amince da sata da kashe-mu-raba ba.
Hausawa sun ce zaman lafiya ya fi zama dan sarki. Babu abin da ya fi lafiya da zaman lafiya alfanu a rayuwar al’umma. A yayin da muka kuduri fitowa daga gidajenmu gobe da nufin zabe, mu tuna da cewa tsawon shekara shida a kasar nan, muna zaune ne cikin rashin tabbas, cikin tsoro da barazana. Kada mu mance da yadda kasarmu ta zama sansanin zubar da jinin bayin Allah, yadda aka zura wa wasu tsiraru ido, suna halaka mana al’umma a kullum. Kada mu mance da yadda aka kashe mana shugabnnin addini, sarakuna, yadda aka kashe mana mata da yara da tsoffi.
Kada fa mu ce za mu mance da yadda ’yan ta’adda suka sace mana mata, musamman ma matan Chibok sama da 200 da aka sace, har yau kusan shekara daya ke nan babu amo babu labari. Kada mu mance da yadda aka kashe mana Malam Albani da sauran malamai nagartattu. Kada mu mance da yadda aka kai wa Shaikh dahiru Bauchi hari, yadda aka kai wa Janar Buhari hari, yadda aka kashe wa Shaikh Zakzaky ’ya’ya uku ringis. Kada mu mance yadda aka samu masallata a Masallacin Jumu’a, a Kano, aka tayar musu da bama-bamai, aka kuma bude musu wuta. Mutane suka mutu, wasu suka tagayyara, wasu suka wulakanta. Kada mu mance da yadda aka rika tayar da boma-bomai a coci-coci, ana kashe mabiya da yawa.
Mu tuna yadda aka babbake hanyoyinmu da sojoji, suna wulakanta al’ummarmu, suna cin zarafinmu, suna amshe mana dukiya. Don haka, idan mun tashi kada kuri’a, mu zabi mutumin da zai tsaya tsayin daka, ya magance mana tashin hanalin nan. Mu zabi mutumin da zai yi amfani da basirarsa, da hikimarsa da jaruntakarsa wajen taka wa tsagerun nan birki. Mu zabi mutumin da zai inganta harkoki tsaro, wanda zai ba sojojinmu da ’yan sandanmu kyakkyawar kulawar da ta kamace su, yadda za su maida hankali ga ayyukansu na samar da tsaro da bin doka da oda.
A yayin da muke shirin zaben sabon Shugaban kasa gobe, lallai ne mu tuna da yadda matasanmu maza da mata ke zaman kashe wando, babu aikin yi balle sana’a. Mu tuna yadda a kullum makarantu da kwalejoji da jami’o’i ke yaye dalibai, amma babu aikin yi. Mu tuna yadda Hukumar Shigi-Da-Fici ta tara matasa da yawa, ta amshe musu kudi da nufin wai za ta ba su aiki. Daga karshe dai a sakamakon turmutsitsi, matasa maza da mata kusan ashirin suka rasa rayukansu, da yawa kuma suka samu raunuka daban-daban. Babu shakka, madamar muna son a kawo gyara a irin wannan abin takaici, to lallai ne mu zabi shugaban da ya dace, mai kishin al’umma. Mu zabi shugaban da zai tabbatar da an farfado da masana’antu, an inganta harkar noma da kiwo, an inganta kasuwanci da sauran kafofin samar da dukiya, ta yadda matasanmu za su samu ayyukan yi da sana’o’i domin dogaro da kai.
Gobe idan Allah Ya kai mu, a yayin da aka lika mana tawwadar zabe a hannu, mu tuna da yadda al’mauran wutar lantarki suka durkushe. Mu tuna yadda kamfanin wutar lantarki ke barinmu cikin duhu a kullum, sannan kuma duk wata yake amsar mana kudi. A sakamakon rashin wutar nan, kamfanoni sun durkushe, harkokin ci gaban kasa sun balbalce. kere-kere da kimiyya sun shiga garari, a sakamakon rashin wutar lantarki. Madamar muna son canji, lallai ne mu kada kuri’armu ga mutum mai kishi da son ganin al’umma ta ci gaba. Mu zabi wanda zai ceto al’umma daga hannun azzalumai, dillalan janareto. Mu zabi mutumin da zai tabbatar da cewa an inganta hanyoyin samar da wutar lantarki, domin bunkasa kasarmu.
Idan mun lura, hanyoyin kasarmu sun lalace, sun balbalce, kullum sai hadurra ake yi, ana sarar rayuka saboda rashin kyawun hanyoyi. Makarantunmu kuwa sun zama tamkar makarantar Jatau-Na-Albarkawa, babu kyau, babu kayan koyarwa, ga yawan yajin aiki. Wannan ta sanya ’yan Najeriya na tafiya Ghana da Nijar wai domin neman ilimi. Mu tuna da yadda asibitocinmu suka lalace, babu kwararru da wadatattun likitoci, babu kayan aiki. Abin takaici, masu mulkinmu, ko ciwon kai suka ji, sai su tsallake zuwa kasashen Turai a duba su.
Madamar muna son ganin karshen nirin wadannan wulakanci, madamar muna son ganin cewa an samu hanyoyi ingantattu, an samu bunkasa harkar ilimi da harkar lafiya, to ya zama wajibi mu zabi mutumin kkirki, mai kishinmu, wanda zai ririta dukiyarmu domin samar mana da inganci.
A zaben namu na gobe, ’yan takara biyu ne kacal masu tasiri, daga mai ci a yanzu, Goodluck Jonathan sai kuma Janar Muhammadu Buhari. Tarihi dai a bayyane yake na ko wane ne Jonathan. Yau dai shekara shida cur yana kan mulki, kuma mun ga yadda al’amura suka kasance a karkashin mulkinsa. Shi kuma Janar Buhari, babu wanda bai san shi ba, babu wanda bai san yanayinsa ba. Mutum ne da makiyansa ma sun yi shaida kan iya aikinsa da kishin kasarsa da al’ummarsa. Cikinsu, wa za ka zaba ya yi maka maganin matsalolinka?
Allah Ya sa a yi zabe lafiya kuma a kammala cikin lumana da kwanciyar hankali, tare da fatan samun muzakkarin shugaban da zai kawo mana canji mai alfanu ga kasarmu, amin!