‘A zurfafa bincike kan rikicin Fulani da Makiyaya’
Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah na kudancin Kaduna, Alhaji Abdulhamid Musa Albarka ya yi kira ga gwamnati da a duk lokacin da aka yi wani rikici ta rika bincika musabbabin abin da ya haifar da rikicin, domin sau da yawa rikici kan faru ne kan wani abu daban, amma nan da nan sai […]
Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah na kudancin Kaduna, Alhaji Abdulhamid Musa Albarka ya yi kira ga gwamnati da a duk lokacin da aka yi wani rikici ta rika bincika musabbabin abin da ya haifar da rikicin, domin sau da yawa rikici kan faru ne kan wani abu daban, amma nan da nan sai a sanya masa rigar addini,wanda hakan ke sa abubuwan su dada kazancewa.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya na kudancin Kaduna a garin Kafanchan.
Game kuma da wata kasida da wata kungiyar Mutanen Kudancin Kaduna, (SOKAPU), suka taba rabawa manema labarai kan rashin amincewarsu da samar da wuraren kiwo na zamani a yankin, ya ce rashin sanin alfanun hakan ne ya sa, amma da sun sani yin hakan shi zai taimaka wajen magance matsalolin da suke korafi a kai na lalata musu amfanin gona kamar yadda suke cewa, domin ta hanyar hakan za a killace Bafulatani a waje daya ta yadda in har ya ketara iyakar da aka killace masa ya shiga gonar wani da dabbarsa, an san shi ke da laifi ke nan. “Sun fi so a bar Bafulatani a haka ne don su ci gaba da cewa ana shiga musu gona?,” inji shi.
Shugaban ya kuma bayyana cewa samar da irin wadannan wurare, baya ga magance matsaloli zai kuma taimakawa Fulani wajen koya musu kiwo irin na zamani ta yadda koda Bafulatani bai da shanu masu yawa za a koya masa yadda zai samu amfani mai yawa daga gare su.
Da yake tsokaci kan rikicin da ya faru kwanan baya tsakanin Fulani da wasu kabilu a yankin Godogodo ta karamar Hukumar Jama’a, shugaban ya bayyana takaicinsa kan yadda “jami’an tsaro suna ji suna gani washegarin rikicin suka bar wats kabilar suka kana rugagen Fulanin da ke yankin. Bai kamata a rika barin mutane na daukar doka a hannunsu ba, kuma a gaban jami’an tsaro ba domin hakan, ba sharewa wasu hawaye ba ne sai dai koyawa wasu yadda ake take doka,” inji shi.
Daga nan ya yi kira ga jami’an tsaro da su ci gaba da zama masu kare rayuka da dukiyoyin al’umma wanda shi ne babban aikinsu.
Har ila yau, ya yi kira ga ’yan uwansa makiyaya da kuma manoma da su zamo masu hakuri da juna tare da bin doka kuma su ci gaba da tattaunawa da sauran kabilun kamar yadda suka saba domin sarakunansu da hakimansu da kuma dagatansu duka suna ba da hadin kai, matsalar daga wajen matasa take tasowa galibi, kamar yadda ya bayyana.
A karshe ya karkare da yin kira ga gwamnati da ta rika sa ido a duk sadda wani abu ya faru a rika yin bincike sosai kada a rika la’akari da dokin mai baki, wanda aka ce ya fi gudu don kada a karshe wanda ake zalunta a dauke shi a matsayin azzalumi shi kuma mai zalunci a dauka shi ake zalunta, kamar yadda ya bayyana. Har ila yau, ya jinjinawa kwamandan yanki na ’yan sandan kudancin Kaduna wato (Kafanchan Area Command), AC Ibrahim Abdullahi kan yadda yake fadi tashi da hana kanshi bacci duk lokacin da aka ce ga wani abu na faruwa a yankinsa.