Ana shirin sako ’yan bindiga, sun kai sabbin hare-hare a Kastina
’Yan ta’adda sun kashe mahalarta ɗaurin aure sun sace amarya da wasu mutane 16 washegarin da gwamnatin jihar ta bayyana dalilan shirinta na sako mutum 70 da ake zargi da ta’addanci a jihar
Taswirar Jihar Katsina
’Yan bindiga sun kai sababbin hare-hare inda suka kashe mutane uku tare da sace wata amarya da mahalarta daurin aure a yankin Karamar Hukumar Katsina ta Jihar Katsina.
An kai wadannan hare-hare ne a yayin da gwamnatin jihar ke shirin sako wasu mutum 70 daga cikinsu wadanda ake tsare kan zargin ayyukan ta’addanci.
A ranar Lahadi da dare ne ’yan bindiga suka kai hari kan jerin gwanon motocin mahalarta ɗaurin aure, tare da kashe aƙalla mutane biyu tare da sace wasu 17, ciki har da amaryar, a yankin Unguwar Nagunda da ke ƙaramar Hukumar Ƙanƙara ta jihar. Daga bisani mutum 8 daga cikin waɗanda aka sace sun tsere inda suka koma wurin iyalansu a ranar Litinin.
Mazauna kauyen Unguwar Nagunda sun bayyana wa wakilinmu jiya cewa ’yan bindiga sun kai hari kan mahalarta daurin auren ne bayan sun iso kauyen.
- Ba wa sojoji aikin tsaron cikin gida na karya gwiwar ’yan sanda — Buratai
- NAJERIYA A YAU: Zabukan Da Aka Gudanar Lokacin Dawowar Mulkin Farar Hula A Jamhuriya Ta Hudu
Wata majiyar tsaro ta shaida cewa jami’an tsaro sun riga sun fara aikin ceto, inda ake ci gaba da yi wa dazuka da wurare masu nisa a cikin jihar bincike domin kubutar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su a yankin Kankara da kewaye.
Kazalika ’yan bindiga sun kashe wani mutum a ƙauyen Kafa da ke kan babbar hanyar Kankara– Sheme da ka ƙaramar hukumar.
An kai waɗannan hare-haren wane washegarin da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasir Muazu, ya bayyana dalilan gwamnatin jihar a shirinta na sakin wasu mutane 70 da ke tsare kan ayyukan ta’addanci a jihar.
A hirarsa da kafar yada labarai ta DLC Hausa, Kwamishinan ya bayyana cewa mutanen da ake shirin sakowa suna fuskantar shari’a ne bisa tuhumar su da aika laifuka masu alaƙa da ayyukan ’yan bindiga.
A cewarsa, za a sake su ne domin ƙarfafa yarjejeniyar zaman lafiya da al’ummomi suka kula da ƙungiyoyin ’yan bindiga a sassan jihar.
A hirarsa da BBC kuma, kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kafa kwamitin tantance sunayen ’yan bindigar da ke tsare domin gabatar da su a kotuna. ba a hakikance adadin ’yan bindigar da za sako ba, amma gwamnatin. Sai dai ya ce ba a kai ka tabbatar da adadin ’yan bindigar da za a sako ba.
Wani mazaunin yankin Jaga ya ce,”Ko da yake muna jin daɗin zaman lafiya mai rauni, amma ’yan bindiga sun fara dawowa.”
Ya ƙara da cewa, a nan yankin ana zargin cewa maharan na daga cikin ’yan bindiga masu adawa da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a kauyen Kakumi na ƙaramar hukumar Bakori, inda ƙananan hukumomi biyar suka shiga— Kankara, Malumfashi, Kafur, Funtua da Bakori mai masaukin baki.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasir Muazu, ya tabbatar da hare-haren.
Mazauna Kankara ke yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ƙara shiga tattaunawa da ’yan bindiga, tare da roƙon a ƙara tura jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.