Ababen da ke magance matsalar qurajen fuska da fata
Assalamu alaikum masu karatu tare da fata nana lafiya? Bari in yi muku wata tambaya. Shin mene ne wadannan abubuwan da ke magance matsalolin fata? Lallai wadannan abubuwa ne, wanda a kullum mukan yi amfani da su a dakin girki ko kuma amfani da su a abinci. Idan aka koyi yadda ake amfani da su […]
Assalamu alaikum masu karatu tare da fata nana lafiya? Bari in yi muku wata tambaya. Shin mene ne wadannan abubuwan da ke magance matsalolin fata? Lallai wadannan abubuwa ne, wanda a kullum mukan yi amfani da su a dakin girki ko kuma amfani da su a abinci. Idan aka koyi yadda ake amfani da su a fata, domin magance matsalolin fata, lallai ba sai an kashe kudi da dama ba wajen sayen magani. Ina son in gargadi masu karatu da su gane cewa a cikin abubuwan da zan lissafo, daya kawai ake so a riqa amfani da shi wanda ta dace da fatar mutum. Amfani da su gaba daya na qara haifar da wata matsalar fata. Yana da kyau a gwada amfani da su tsawon watanni biyu zuwa uku.
• Domin magance matsalar fata mai yawan saba ko masu samun barewar fata daga fuskarsu ko wata bangare a fatar jiki, sai a samu suga mai launin qasa da zuma da madara kadan yadda sugan ba zai narke ba, sai a shiga dirzawa a fuska ko wani bangaren da matsalar ta shafa.
• Qarin haske: idan fuska ta kasance tana yin baqi a sakamakon yawan fita rana ko kuma canjin yanayi, yana da kyau a kwaba ayaba, sannan a hada da zuma da kuma lemun tsami sai a riqa shafawa a qalla sau biyu a rana na tsawon mintuna ashirin kafin a kwanta barci.
• Sheqin fata: samin fatar fuska mai sheqi, sai an dage da cin kankana da kuma kwabata da cokali sannan a riqa shafawa a fuska ko jiki na tsawon mintuna talatin a qalla sau biyu a rana sannan a wanke.
• Tsagewar lebe: Iidan lebe na yawan tsagewa ko kuma bushewa, sai a samu man kwakwa da siga sai a dan diga man kwakwa da sukari kadan, sannan a shiga dirza sukari a lebe na tsawon mintuna biyu zuwa uku, sannan a wanke. A kasance yawan shafa man kwakwa a leben.
• Gautsin fata: gautsin fata na hana fata sheqi. Don haka, yana da kyau a kasance amfani da fiya da ruwan lemun zaqi. A kwabasu waje daya sannan a riqa shafawa a waje mai gautsin domin magance matsalar.
• Fesowar quraje: a kasance amfani da ruwan qwai ban da gunduwar sannan a riqa shafawa a fatar fuska a kullum na tsawon mintuna ashirin zuwa ashirin da biyar kafin a wanke sau biyu a rana domin samun biyan buqata.