Ababen da ke saurin sanya tsufar fuska

Fata na daya daga cikin ababen da ke dada wa mace kyau, domin in har ana da fata mai kyau, ko ba ayi kwalliya ba sai aga anyi kyau  don haka, fata na da matukar mahimmanci a jiki, don haka dole ne mu kula da ita. Akwai ababe da dama wadanda ya kamata ayi la’akari […]

Ababen da ke saurin sanya tsufar fuska

Fata na daya daga cikin ababen da ke dada wa mace kyau, domin in har ana da fata mai kyau, ko ba ayi kwalliya ba sai aga anyi kyau  don haka, fata na da matukar mahimmanci a jiki, don haka dole ne mu kula da ita. Akwai ababe da dama wadanda ya kamata ayi la’akari da su domin rage tsufar fata kamar haka; 

• Yawan goge fuska da ruwan goge fuska (cleanser) na sanya tsufar fuska. Idan ana da fata mai gautsi, to ya kamata a wanke fuska da sabulu da ruwa kawai kafin a kwanta bacci ba tare da an sanya wa fuska cleanser ba.

•Yawan dirza fuska da karfi idan an zo wanke ta na janyo fesowar kurarraje a fuska da kuma dada tsufar fata. Fata na so a lallaba ta. Saboda haka, ya kamata  a rika liliya fatar kamar na jinjiri. Ko da ana wanke ta da sabulu ne.

• Amfani da mayuka masu dauke da sinadarin (sunscreen) na da mahimmanci sosai. Domin, wannan irin man na kare fuska daga kunar rana. Don haka dole ne mu sami man da ke dauke da irin wannan sinadarin domin rage tsufar fuska ko hana ta tsufa.

• Yawan kwanciya a kan hannu a benci musamman ga ma’aikata na sakar da fatar ta yi sakwa-sakwa. Idan ana da irin wannan halin to dole ne a rage in har ana son a kula da fatar fuska da na jiki.

• Yawan amfani da tsinkin shan lemu (straw) na sakar da fatar baki. Domin bakin zai kasance kulum cikin tsotsa. Sai a ga fatar bakin ta fara fitar da layuka hakan na haifar da tsufar fatar bakin.

• Kada a manta da motsa jiki domin hakan na taimaka wa jinin jikinmu wuce wa ba tare da wata takura ba. Idan ko jinin jiki na wuce wa da kyau za a ga fatar jiki na fito wa bulbul. Yana da kyau a rika motsa jiki na misalin minti 30 a kullum domin samin lafiyar jiki.