Ababen da ya kamanci jakar kwalliya

Shin me ake sawa a jaka wadda kullum ba a rasa ta da su? Ina fatan ’yan mata na da jakar kwalliya. Ko me ce ce jakar kwalliya? Jakar kwalliya karamar jaka wacce za ki iya adana kayan kwalliyarki kamar su; jambaki, gazal, hoda da sauransu. Akwai abubuwa da dama wanda ya cancanta ki sanya […]

Ababen da ya kamanci jakar kwalliya

Shin me ake sawa a jaka wadda kullum ba a rasa ta da su? Ina fatan ’yan mata na da jakar kwalliya. Ko me ce ce jakar kwalliya? Jakar kwalliya karamar jaka wacce za ki iya adana kayan kwalliyarki kamar su; jambaki, gazal, hoda da sauransu. Akwai abubuwa da dama wanda ya cancanta ki sanya a jakar kwalliyarki don inganta adonki. Amfani da jakar kwalliya wajibi ne ga matar zamani domin kuwa wata ba za ta ganu ba in ba bu wannan kwalliyar ita kwalliyar ce ke rufe mata tabon da ke fuskarta ko kuma kurajen fuska. In har ba ki da ita ya kamata ki samu daya. A yau na kawo maku kadan daga ciki;

• Concealer: tana taimakawa wajen boye bakaken da ke fuskarki. A kan shafa ta ne bayan an sanya hodar fandesho.

• Maskara: A kan yi amfani da ita don taje gashin ido da kuma sanya masa kala. Akwai sabbin kaloli na maskara a kasuwa wanda za ki iya saya don kara wa gashin idonki kyau.

• Gazal: Sanya gazal a idanunki don karawa idanunki haske. Gazal na taimakawa wajen sanya hasken idanu.

• Jan baki/man baki: Yana kara kyau da kuma sanya wa labba laushi. Ki zabi jan bakin da ya dace da kalar fatarki domin inganta adonki.

• Fandesho: Amfanin wannan shi ne, bayan mace ta yi alwala kwalliyarta zai wanku musamman idan tana da kurajen fuska. Wannan fandesho amfaninsa shi ne ya boye wadannan tabon kurajen fuska. Don haka yana da mahimmanci a samu fandesho a jakar kwalliyar mace. Hodar kuma na dada hasken fata.

• Hoda: Ita ma tana da muhimmanci a same ta a jakar mace domin bayan an shafa fandesho, takan shanye gumin fuska da kuma sanya kwalliyar ta zama sabuwa kamar na yadda aka yi ta da safe. Akwai nau’ukan hoda masu dauke da sinadaran kashe kurajen fuska su ma suna taimakawa wajen warkar da wadannan kurajen.