Abacha: Hatsabibin ɗan Boko Haram ya miƙa wuya ga sojoji

Abacha ya miƙa wuya biyo bayan ruwan wuta da sojoji ke musu.

Abacha: Hatsabibin ɗan Boko Haram ya miƙa wuya ga sojoji

Dakarun Haɗin Gwiwa na Ƙasashe (MNJTF), sun bayyana cewa wani hatsabibin ɗan ta’addan Boko Haram mai suna Bochu Abacha, ya miƙa wuya ga sojoji a Jihar Borno.

Jami’in Yaɗa Labaran Rundunar, Laftanar Kanal Olaniyi Osaba ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a Maiduguri, a ranar Asabar.

Osaba, ya ce Abacha, wanda ya yi fice wajen ayyukan ta’addanci da dama, ya amsa cewar ya jagoranci kai wasu hare-hare a yankin Monguno zuwa Baga.

Ya bayyana cewa Abacha ya ce ya miƙa wuya ne saboda hare-haren da rundunar ke kai wa Boko Haram.

Yayin da ya miƙa wuya, Abacha ya bayar da bindigarsa ƙirar AK-47, ƙunshin alburusai, waya, layin waya na Airtel, da kuma kuɗi Naira 32,500.

Osaba, ya ce yanzu haka Abacha yana bayar da muhimman bayanai ga hukumomin tsaro a jihar.

A wani samame daban, sojojin MNJTF tare da jami’an leƙen asiri suka kai wa Boko Haram, sun yi nasarar kashe ɗaya tare da raunata wasu, sannan suka fatattaku sauran.

Osaba, ya ce daga cikin kayayyakin da suka gano akwai motoci guda uku cike da kayan abinci da wasu kayayyaki kuma Naira N2,000.

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou