Abaya: Yadda gasar kayan Sallah ke sanya mata a hadari
Yadda gasar sanya abaya ta #AbayaChallenge ke nemar tayar wa ’yan mata zaune tsaye.
Gasar sanya Abaya ta #AbayaChallenge ta sa ’yan mata rokon samari su saya musu ita a domin kece raini a lokacin bikin Karamar Sallar bana.
Gasar ta da ke tashe a kafafe sada zumunta ta kara wa ’yan mata hankoronsu na shiga cikin tsara ta hanyar yin ado da Abayar a Karamar Sallar da ake shirin yi nan da ’yan kwanaki.
Aminiya ta gano cewa lamarin na #AbayaChallenge na neman jefa ’yan matan cikin hadari.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa a yanzu haka, burin’yan matan na sanya Abaya ta kai su ga rokon samarinsu su saya musu ita a matsayin toshin kayan Sallah.
Bayanai sun kuma nuna cewa wadansu samari na cewa sai dai a yi ba-ni-gishiri, in-ba-ka manda tsakaninsu da ’yan matan kafin su saya musu ita.
Har ta kai samarin suna yi wa abin take da “In ba ki Abaya ki ba ni abaya.”
Hattara dai mata – Malama Zahra’u
Wannan ne ya sa Kwamishinar Mata ta Jihar Kano, Malama Zahra’u Muhammad Umar ta yi kira ga iyaye su sanya idanu kan ’ya’yansu mata musamman wadanda samarinsu suka kawo musu kyautar Abaya.
Malama Zahra’u ta kuma ja hankalin samarin da ’yan mata da su ji tsoron Allah tare da kiyaye dokokinSa, kada su yi abin da shari’a ta hana.
#AbayaChallenge ta canja salon dinki
Binciken Aminiya a Kano ya gano cewa Abaya ta zama suturar da mata za su fi amfani da ita a Karamar Sallar bana, inda ta kai ga ana yi wa kwalliyar ta bana take da Kalubalen Abaya, a shafukan sada zumunta.
“Idan mace ba ta sa Abaya a Sallar bana ba, ba ta cika mace ba,” wata budurwa mai suna Yahanasu Sani ta shaida wa Aminiya.
Yahanasu ta ce a yanzu kwalliya ko salon dinkin mata gaba daya ta koma ga doguwar riga, “Idan kin kula ba ma dinkin Abaya ba, ko salon dinkin da ake yi na atamfa da leshi da shadda sun koma doguwar riga ba kamar yadda aka saba dinka zane da riga ba,” inji ta.
Abin bai tsaya ga manyan mata kawai ba, hatta yara mata ba a bar su a baya ba wajen burin yin ado da Abaya a lokacin Sallah ba.
Lubabatu Muhammad da aka fi sani da Maman Hafis ta shaida wa Aminiya cewa ’ya’yanta mata biyu sun dame ta kan lallai sai ta yi musu Abaya, “Wai an fada musu duk macen da ba ta sa Abaya a Sallar ba kwalliyarta ba ta cika ba.
“Abin takaici shi ne na sha yawo a kasuwa amma ban samu wacce za ta yi musu ba, kin san Abayar an fi yin ta manya. Amma yanzu na samu wata tela za ta dinka musu,” inji ta.
Rige-rigen sayen Abaya
Aminiya ta zagaya Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano inda ta ga cincirindon mata a wajen masu sayar da Abaya.
Malama Hafsa Adamu, daga cikin matan da ke bin layin sayen Abaya, ta shaida wa Aminiya cewa ta zo saya wa ’ya’yanta Abaya ne saboda sun shaida mata ita suke so.
“Ni dai ban san wane abu ake ya yi a gari ba, ’ya’yana ne kawai suka fada min cewa su Abaya suke so a saya musu a Sallar bana.
“Na yi zaton ma don ba su son zuwa wurin tela ne saboda guje wa cunkoso,” inji ta.
Rokonmu ake mu karbi aiki – Telolin Abaya
Sai dai wani binciken ya gano cewa a yazu teloli sukan dinka Abayar.
Sadik Muhammad telan Abaya ce a Kasuwar Sabon Garin Kano, ya bayyana cewa tun kafin azumi shagonsa ke cike da kayan dinki wanda a yanzu haka ma ba zai iya kammala dinka kayan da ke gabansa ba kafin Sallah.
Zaliha Sani Abubakar telar Abaya ce, ta ce a yanzu haka aikin da ke gabanta ya yi mata yawa sakamakon bukatar da mutane ke da ita ta Abayar.
“Kin ga kamar bara da Sallah ta zo ba mu yi dinkin ba. Amma bana sai ga shi abin ya canja sakamakon bukatar da mutane ke da ita ta rigunan Abaya.
“A kullum kawo min dinki ake yi, idan na ki karba a yi ta rokona,” inji ta.
Sai dai a binciken da Aminiya ta gudanar a Kasuwar Kantin Kwari ya gano duk da cewa matan sun mayar da hankali kan neman Abaya a matsayin kayan Sallah, a gefe guda akwai matan da ke sayen atamfa da leshi da shadda da saurasnu.
Game da farashin, Abaya ya danganta da yanayin yadi da kuma dinkin da aka yi mata. Akwai Abayar Naira dubu uku har zuwa ta Naira dubu 50.