Abba El-Mustapha ya samu lambar yabo kan yaƙi da cin hanci
Jarumin na Kannywood ya yi alƙawarin ci gaba da yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar.
Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Jihar Kano, ta karrama Shugaban Hukumar Tace Fina-finai na Jihar, Abba Al-Mustapha, kan gwagwarmayarsa wajen yaƙi da cin hanci.
Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar tace fina-finai, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar a ranar Talata.
Ya bayyana cewa jajircewar Al-Mustapha wajen yaƙar cin hanci da rashawa, ita ta sa aka ba shi wannan lambar yabo.
Shugaban Hukumar Karɓar Koke-koke, Muhuyi Magaji Rimingado ne, ya miƙa wa Abba Al-Mustapha, lambar yabon.
Da yake jawabi, Al-Mustapha, ya yi wa hukumar bisa wannan karamci da ta masa.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙari wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, wanda ya ce na ɗaya daga cikin matsalolin da ke kawo koma baya ga tattalin arziƙin ƙasa.
Kazalika hukumar ta karrama wasu a wajen taron, duba da irin gudunmawar da suka bayar wajen daƙile cin hanci da rashawa a jihar.