Abba El-Mustapha ya zama shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa tauraron Kannywood, Abba El-Mustapha a matsayin Sakataren Gudanarwa na hukumar tace fina-finai ta jihar. Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da wannan naɗin a ranar Litinin. Abba El-Mustapha wanda ake yi wa taken “Abba na Abba” saboda kusancinsa da gwamnan ya maye gurbin Alhaji […]

Abba El-Mustapha ya zama shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa tauraron Kannywood, Abba El-Mustapha a matsayin Sakataren Gudanarwa na hukumar tace fina-finai ta jihar.

Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da wannan naɗin a ranar Litinin.

Abba El-Mustapha wanda ake yi wa taken “Abba na Abba” saboda kusancinsa da gwamnan ya maye gurbin Alhaji Isma’ila Na’Abba Afakallah.

Ina da kyakkyawar alaka da ’yan fim  – Afakallah

Ba za mu raga wa wanda ya karya doka ba – Afakallah

An dai kafa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ne domin ɗora fina-finai da littattafan Hausa bisa tafarkin adddini da al’adar al’ummar Kano.

Sai dai hukumar ta yi ƙaurin suna wurin kama ƴan Kannywood musamman masu adawa da gwamnatocin dake mulki a jihar.