Abba Gida-Gida ne Gwamnan Kano — Kotun Ƙoli

Wannan dai ya kara tabbatar da cewa Gawuna ba zai zo ba ke nan.

Abba Gida-Gida ne Gwamnan Kano — Kotun Ƙoli

Kotun Ƙolin ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar Kano.

Da wannan mataki, kotun ta yi watsi da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke na tsige gwamnan daga mukaminsa.

Alkalai biyar da suka yanke hukuncin na bai ɗaya, sun ce Kotun Daukaka Karar ta yi kuskure wajen zaftare wa Abba Yusuf kuri’u 165,617 saboda rashin hatimin Hukumar Zabe ta Kasa INEC a kan takardun da aka kada masa kuri’a.

Alkalin da ya jagoranci hukuncin na wannan Juma’ar a zauren Kotun Ƙolin da ke Abuja, Mai Shari’a Inyang Okoro, ya ce takaddamar kasancewar Gwamna Abba dan jam’iyyar lamari ne da kotu ke da hurumin sauraronsa kaɗai gabanin zabe.

Mai Shari’a Inang ya bayyana cewa, dalilai da aka gabatar bisa la’akari da sashe na 177 (c) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da sashe na 134(1) na Dokar Zabe da ke cewa Abba Yusuf ba dan jam’iyyar NNPP ba ne, dalilai ne kawai na hasashen cewa babu sunansa a cikin jerin membobin jam’iyyar ba tare da Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta tabbatar da hakan ba.