Abba Gida-Gida ya gargadi gidajen mai a kan kara farashi

Gwamnan ya ce har yanzu gidajen man suna da man da suka sayo a tsohon farashi, a don haka ya ce kamata ya yi su sayar da shi a tsohon farashi.

Abba Gida-Gida ya gargadi gidajen mai a kan kara farashi

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya bukaci masu gidajen man fetur da su rika sayarwa a kan tsohon farashi, maimaikon yadda suke sayarwa yanzu, domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta a jihar.

Gwamnan ya ce yana sane da cewa har yanzu masu gidajen man suna da man da suka sayo a tsohon farashi, a don haka ya ce kamata ya yi tunda tsohon kaya ne, a sayar da shi a tsohon farashi.

Sanarwa da Babban Sakataren Yada labaran gamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, ta ce, “A matsayina na Gwamnan da ya damu da halin da jama’arsa suke ciki, ba na jin dadin ganin yadda jamar jihar ke shan wahala saboda wannan karin kudin man da ba ta bisa kaida, don haka dole ne a dakatar da wannan lamari ba da bata lokaci ba.”

A cewar Gwamna Abba, ganin cewa Jihar Kano cibiyar kasuwanci ce wadda dimbin mutane ke amfana da ita a fadin Afrika ta Yammaa, zai yi duk abin da ya dace wajen ganin al’umma sun ci gaba da more wannan baiwa da Allah Ya huwace wa jihar.

Gwamnan ya yi kira ga alummar jihar da su kwantar da hankulansu tare da bin doka da oda saboda gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa al’umma suna ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda suka saba.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya