Abba Gida-Gida ya gayyaci Sanusi II bikin rantsar da shi
Sai dai babu tabbacin ko zai halarci wajen ko a’a
Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gayyaci tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II zuwa wajen bikin rantsar da shi a ranar Litinin mai zuwa.
A cikin wata wasika da Abban ya sanya wa hannu da kansa mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Mayun 2023, wacce Aminiya ta gani, Gwamnan mai jiran gado ya ce halartar Sanusi ba wai kawai za ta kara wa bikin armashi ba ne, za kuma ta kara wa goyon bayan da suke da shi a wajen jama’a.
- An tsaurara matakan tsaro a Abuja gabanin rantsar da Tinubu
- Mika Mulki: Buhari ya zagaya da Tinubu fadar shugaban kasa
Wasikar ta kuma ce, “Na san kana sane da cewa an gudanar da zaben Gwamnan Jihar Kano ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata, wanda Allah (SWT) Ya kaddara na yi nasara, kuma daga bisani Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba ni shaidar lashewa.
“A kan haka ne nake gayyatarka zuwa wajen bikin rantsar da ni wanda za a yi ranar Litinin tare da Mataimakina, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo,” in ji wasikar.
Sai dai wani fitaccen mamba a kwamitin karbar mulki na Jihar wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin yin magana da ’yan jarida ya tabbatar da cewa sun yanke shawarar gayyatar dukkan fitattun mutane ’yan asalin Jihar ne.
Ya ce la’akari da hakan ne tare kuma da cewa kotu ta dage haramcin da aka sanya wa tubabben sarki na ziyartar Jihar, ya sa ba zai yi mamaki ba idan aka gayyace shi.
Shi ma wani makusancin Sanusin, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da cewa Sanusin, amma bai kai ga yanke shawarar ko zai halarci wajen ba ko kuma a’a.
Ya ce dalili kuwa shi ne an gayyace shi wuraren rantsuwa har guda biyu; ta Shugaban Kasa da kuma Gwamnan Abiya.
Sai dai ya ce Halifan a Darikar Tijjaniya ya bar Najeriya zuwa kasar Afirka ta Kudu da yammacin Juma’a.