Abba Gida-Gida ya naɗa sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Kano
An tabbatar da kwarewarsa a ma’aikatun gwamnatin Kano daban-daban da ya yi aiki tsawon shekaru fiye da talatin.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano.
Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Harkokin Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a wannan Litinin din.
- Kotu ta soke zaben Kakakin Majalisar Kaduna
- Dole mu dage wajen kare darajar bangaren shari’a — Alkalin Alkalai
Hakan dai ya biyo bayan ajiye aiki da tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Kano, Alhaji Usman Bala mni ya yi a wannan wata na Nuwamba.
Dawakin-Tofa ya ce sabon Shugaban Ma’aikatan gogaggen ma’aikacin gwamnati ne wanda aka tabbatar da kwarewarsa a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin Kano daban-daban da ya yi aiki tsawon shekaru fiye da talatin.
Alhaji Abdullahi wanda ya fito daga Karamar Hukumar Kiru, ya yi aiki a fannoni da dama ciki har da Babban Sakatare a Fadar Gwamnatin Kano, Cibiyar Kula da Harkokin Gwamnati, Ma’aikatar Ayyuka na Musamman da Hukumar Servicom.
Ya samu shaidar digiri na farko a fannin nazarin harkokin diflomasiyya daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Haka nan, ya samu shaidar digiri na biyu a fannin Tsare-Tsare da Gudanarwa daga Jami’ar Bayero da ke Kano, da kuma karin wata shaidar digiri na biyu a fannin nazarin Dabarun Tsaro a Harkokin Gudanarwa daga Makarantar Horas da Dakarun Soji (NDA) da ke Kaduna.
Sanarwar ta kara da cewa, Gwamna Abba Yusuf wanda ake yiwa lakabi da Abba Gida-Gida, ya buƙaci sabon Shugaban Ma’aikatan da ya sauke nauyin da rataya a wuyansa bisa la’akari da tsare-tsare da dokokin aikin gwamnati.