Abba Gida-Gida ya nada shugabannin Hukumar Alhazai

Ana sa ran wadanda aka nada za su tabbatar da ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin 2023.

Abba Gida-Gida ya nada shugabannin Hukumar Alhazai

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin sabbin shugabannin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada labaran Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aiko wa Aminiya.

Wadanda aka nada sun hada da Alhaji Yusuf Lawan a matsayin shugaba, sai Alhaji Laminu Rabi’u a matsayin Babban Sakatare.

Haka kuma an nada Sheikh Abbas Abubakar Daneji da Shiek Shehi Shehi Maihula da Amb. Munir Lawan da Shiek Isma’il Mangu da Hajiya Aishatu Munir Matawalle da Dokta Sani Ashir dukkaninsu a matsayin mambobin kwamitin.

Ana sa ran wadanda aka nada za su karbe al’amuran hukumar nan take domin ganin an samu nasarar gudanar da aikin Hajjin 2023.

Hotunan zanga-zangar tsofaffin sojoji Abuja

Girgizar ƙasa ta kashe mutum 95 a ƙasar Tibet

Boko Haram ta mamaye sansanin sojoji ta sace makamai a Borno

Ɗan ta’adda ya sa wa Zamfarawa harajin N100m