Abba Kabir Yusuf na NNPP ya zama zababben Gwamnan Kano

INEC ta bayyana Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin zababben Gwamnan Kano a zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023

Abba Kabir Yusuf na NNPP ya zama zababben Gwamnan Kano

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Injiniya Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin zababben Gwamnan Kano a zaben da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Da yake bayyana sakamakon zaben, Shugaban Tattara Sakamakon Zaben, Farfesa Ahmad Tukur Ibrahim, wanda malami ne a Jamiar Ahmadu Bello da ke Zariya ya bayyana cewa Abba ya yi nasara da kuri’u 1,019,602.

Wanda ya zo na biyu a zaben shi ne Nasir Yusuf Gawuna, na Jam’iyyar APC kuma mataimatin gwamna mai ci, wanda ya samu kuri’u 890,705; tazarar kuri’un da ke tsakanin ‘yan takarar 128, 897, daga ciki kuri’u 2,004,964 da aka jefa a zaben.

Karo na biyu ke nan da Abba ya tsaya takarar Gwamnan Kano, inda a 2019 ya tsaya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.

Sai dai a wancan karon ya sha kaye a hannun Gwamnan Abdullahi Ganduje, a zaben mai cike da rudani.

Abba ya kasance Kwamishinan Ayyyuka a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Kawo yanzu Jihar Kano cewa kadai NNPP ta lashe zaben gwamna, a yayin da INEC ke ci gaba da tattara sakamakon zaben jihohi.

Hakazalika Kano, mahaifar Kwankwaso wanda shi ne dan dan takarar shugaban kasa na NNPP, ta kasance cibiyar jam’iyyar a wannan karon, inda take da sanatoci biyu da kuma ‘yan majilar tarayya da dama.

Aminiya ta ruwaito cewa kawo yanzu APC ta lashe zaben gwamnoni a jihohi takwas, a yayin da PDP ke da hudu.