Abba Kyari na murmurewa — Kwamishinan Lafiya

Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari, yana murmurewa daga cutar  Coronavirus da ya kamu da ita. Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ne ya bayyana hakan lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai ranar Talata a ofishin gwamnati da ke Alausa. Farfesa Abayomi ya ce zuwa yanzu bai san […]

Abba Kyari na murmurewa — Kwamishinan Lafiya

Abba Kyari

Shugaban Ma’aikata a Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari, yana murmurewa daga cutar  Coronavirus da ya kamu da ita.
Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ne ya bayyana hakan lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai ranar Talata a ofishin gwamnati da ke Alausa.
Farfesa Abayomi ya ce zuwa yanzu bai san inda ake bai wa  Malam Abba Kyari kulawa ba, amma sun yi musayar bayanai  da shi ta manhajar WhatsApp.
“Mun tattauna da shi ta manhajar WhatsApp kuma bisa ga dukkan alamu yana samun lafiya, yana murmurewa, amma ban san hakikanin inda yake ba a lokacin da muka tattauna” , inji Farfesa Abayomi.
A makon jiya ne dai aka mayar da Malam Abba Kyari Legas domin ya yi jinya bayan da aka tabbatar cewa yana dauke da cutar Coronavirus.
Ana tunanin jami’in na hannun daman Shugaba Muhammadu Buhari ya kamu da cutar ne yayin wata ziyara da ya kai Jamus, inda ya wakilci gwamnatin Najeriya wajen rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyi.

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a wani sabon hari a Filato