Abba Kyari ya koma gida bayan cika sharuɗan beli

Dakataccen jami’in ya koma cikin iyalinsa bayan shafe sama da watanni 27 a tsare.

Abba Kyari ya koma gida bayan cika sharuɗan beli

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon kwamandan rundunar leken asiri ta ’yan sandan Najeriya, DCP Abba Kyari bayan shafe watanni 27 yana tsare.

An saki Kyari daga gidan gyaran hali na Kuje da ke babban birnin tarayya, Abuja.

A ranar 14 ga watan Fabrairu, 2022, hukumar NDLEA ta kama Kyari, kan zargin alaƙa da wata ƙungiyar miyagun ƙwayoyi.

Hotunan yadda iyalai da ‘yan uwan Kyari suka tarbe shi sun karade kafafen sada zumunta.

Daga cikin yadda aka tarbe shi har da wani rubutu da aka maƙale a bango da “Barka da dawowa.”

NDLEA ta kama Kyari da wasu daga cikin tawagarsa ta ‘yan sanda – Lahadi Ubia, Bawa James, Simon Agirigba, da John Nuhu tare da gurfanar da su a gaban kuliya a ranar 7 ga watan Maris, 2022.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania