Abba ya ƙaddamar da bincike kan zaftare albashin ma’aikatan Kano

Duk wanda aka samu da hannu a wannan mummunan aiki zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Abba ya ƙaddamar da bincike kan zaftare albashin ma’aikatan Kano

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi tsattsauran gargaɗi dangane da rahotannin da ke yawo kan cirar kuɗi daga albashin ma’aikatan gwamnati ko kuma ƙin biyan su gaba ɗaya.

Ya bayyana hakan a matsayin cin zarafin ma’aikata da cin amanar jama’a, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci hakan ba.

Biyo bayan korafe-korafen da ma’aikata suka yi, na cewa wasu daga cikinsu sun shafe watanni ba tare da samun hakkokinsu ba, Gwamna Yusuf ya sha alwashin gano masu hannu a wannan ɗanyen aiki da kuma hukunta su.

“Gwamnatin nan ba za ta yarda da zalunci ma’aikatanta ba. Duk wanda aka samu da hannu a wannan mummunan aiki zai fuskanci hukunci mai tsanani,” in ji Gwamnan.

Gwamnan ya kafa kwamitin bincike mai ƙarfi domin gano musabbabin matsalar, wanda zai gudanar da cikakken bincike kan tsarin biyan albashi daga watan Oktoba 2024 zuwa Fabrairu 2025

An ɗora wa kwamitin alhakin gano ma’aikatan da abin ya shafa, tasirin hakan kan kuɗin gwamnati, tare da ba da shawarwari kan yadda za a magance matsalar da kuma hukunta masu hannu a ciki.

Kwamitin, wanda ke da mambobi bakwai yana karkashin jagorancin Kwamishinan Raya Karkara da Ci-gaban Al’umma kuma tsohon Akanta Janar na Jiha, Abdulkadir Abdussalam.

Mambobin sun hada da: – Abdulkadir Abdussalam – Shugaban Kwamitin kuma Kwamishinan Raya Karkara da Ci-gaban Al’umma da Dokta Bashir Abdu Muzakkari – Mai ba da shawara na musamman kan tattalin arzikin zamani.

Sai Dokta Aliyu Isa Aliyu – Darakta Janar na Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano da Dokta Hamisu Sadi Ali – Darakta Janar na Hukumar Kula da Bashin Jihar Kano da Hajiya Zainab Abdulkadir – Darakta ta Cibiyar Kwamfuta ta Jihar Kano.

Akwai kuma Aliyu Muhammad Sani – Darakta na Bincike da Tantancewa a Ofishin Sakataren Gwamnati da Ummulkulthum Ladan Kailani – Mataimakiyar Sakatariya, Ofishin Sakataren Gwamnati.

An bai wa kwamitin wa’adin kwanaki bakwai domin kammala binciken tare da mika rahoto wanda zai ƙunshi sunayen masu laifi, asarar da aka yi, da kuma shawarwarin magance matsalar gaba ɗaya.