Abba ya ba alhazan Kano 50 da guzurinsu ya bata a Saudiyya kyautar miliyan 6.5
Ya ce ya ba su ne saboda su rage radadin halin da suka shiga
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ba alhazan Jihar su 50 da suka batar da kudaden guzurinsu a kasar Sudiyya kyautar Riyal 30,000 kowannensu.
Shugaban Hukumar Jindadin Alhazai ta Jihar, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a birnin Makka.
- Bidiyon Dala: Kotu ta sanya ranar yanke hukunci kan kama Ganduje
- Bayan shekara 9, kotu ta wanke Sule Lamido da ’ya’yansa daga zargin almundahana
A cewar wata sanarwa da mai rikon mukamin Kakakin Kwamitin Aikin Hajjin bana na Jihar Kano, Nasiru Yusuf Ibrahim, ya fitar ranar Talata, Gwamnan ya ba alhazan tallafin ne saboda su samu su rage radadin halin da suka shiga sakamakon batan kudin.
Laminu Danbappa ya ce tuni kowanne daga cikin alhazan ya samu rabin kudin wanda ya kama daga Riyal 750 zuwa Dalar Amurka 500.
A wani labarin kuma, kwamitin ya ce yana sa ran ya kammala jigilar alhazan Jihar daga kasa mai tsarki a ranar Lahadi mai zuwa.