Abba ya bai wa Hajiya Mariya Galadanchi tallafin N2m
Gwamnan ya ba ta tallafin ne domin kula da lafiyarta.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa fitacciyar mai gabatar da shirin nan na ‘Zabi Sonka’ a gidan Rediyon Kano, Hajiya Mariya Galadanchi, tallafin Naira miliyan biyu.
An ba ta tallafi ne a madadin Gwamnan ta hannun Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Malam Baba Halilu Dantiye, domin taimaka mata wajen kula da lafiyarta.
- Mun mayar da yara miliyan 1.5 makaranta a Borno – Zulum
- Boko Haram sun fille kan masunta 14 a kan iyakar Najeriya
Da yake jawabi yayin ba ta tallafin, Dantiye ya jaddada girmamawa da godiyar Gwamnan kan gudunmawar da Hajiya Mariya ta bai wa al’ummar Jihar Kano.
“Gwamna ya gamsu da jajircewa da sadaukarwar mutane irin su Hajiya Mariya Galadanchi, wadda ta kwashe shekaru 60 tana yi wa al’ummar Kano hidima ta hanyar aikinta a Rediyon Kano,” in ji Dantiye.
“Wannan tallafi na nuni da yadda Gwamna yake jajircewa wajen taimaka wa waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu don ci gaban al’umma, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziƙi.”
Hajiya Mariya, mai shekara 93, ta yi wa gwamnan godiya.
Duk da cewa ta yi ritaya daga aiki, har yanzu tana ci gaba da gabatar da shirin ‘Zaben Abba Gida-Gida’ a Rediyon Kano saboda kishinta na watsa labarai da yi wa al’umma hidima.
“Duk da shekaruna, na ci gaba da gabatar da wannan shiri saboda ƙaunata ga aikin watsa labarai da kuma burina na yi wa jama’a hidima,” in ji Hajiya Mariya.
“Wannan tallafi zai ƙara min ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da bayar da gudunmawa ga ci gaban Jihar Kano.”
Ta kuma yi gwamnan addu’a, inda ta yi fatan Allah Maɗaukakin Sarki ya saka masa da alheri kuma ya ba shi nasara a shugabancinsa.