Abba ya bai wa iyalan ’yan sandan da suka rasu kyautar N5.2m
Gwamnan ya yi addu’ar samun rahama ga waɗanda suka rasu, tare da fatan sauki sauƙi ga waɗanda suka jikkata.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi wa iyalan ’yan sandan da suka rasu a hatsarin mota da ya auku a garin Ƙarfi da ke hanyar Zariya zuwa Kano, tare da ba su kyautar Naira miliyan 5.2.
’Yan sandan sun yi hatsari ne lokacin da suke dawowa daga aikin zaɓen da aka gudanar a Jihar Edo.
- Abacha: Hatsabibin ɗan Boko Haram ya miƙa wuya ga sojoji
- Abba ya ƙaddamar da yaƙi da cutar shan-inna a Kano
Wannan na zuwa ne bayan awanni 12 da ziyarar Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ziyarci iyalan waɗanda suka rasu a ƙaramar hukumar Bichi.
A yayin ziyarar Ganduje, ya bayar da tallafin Naira miliyan 20 domin taimaka wa iyalan da waɗanda suka ji rauni.
Gwamna Yusuf tare da manyan jami’an gwamnatin Kano, sun ziyarci ofishin rundunar ‘yan sandan Bichi domin yi musu ta’aziyya kan rasa abokan aikinsu.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu da rahama, ya kuma bai wa waɗanda suka ji rauni sauƙi.
Gwamnan ya kuma bai wa iyalan kowane ɗan sanda da ya rasu kyautar Naira 500,000, sannan ya bai wa waɗanda suka jikkata kyautar Naira 250,000 kowannensu.
Hukumar Kiyaye Hadura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar da faruwar hatsarin da safiyar ranar Talata.
Ta ce hatsarin ya auku tsakanin wata tirela da wata mota ƙirar Toyota Hummer.
Hatsarin ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkata wasu 10.
Bincike ya nuna cewa gudun wuce ƙima ne, ya haddasa hatsarin, inda direban bas ɗin ta ƙwace masa ya bugi tirelar da aka ajiye a gefen hanya.