Abba ya bai wa Sani Danja muƙamin mai ba shi shawara

Danga ya shiga jerin waɗanda suka rabauta da sabbin muƙamai a gwamnatin Abba.

Abba ya bai wa Sani Danja muƙamin mai ba shi shawara

Fitaccen Jarumin Kannywood, Sani Musa Danja, ya zama Mai Bai wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Shawara kan Harkokin Matasa da Wasanni.

Sanarwar na cikin sauye-sauyen muƙamai da gwamnan ya yi domin inganta harkar gwamnatinsa.

Danja, ya yi fice a harkar fina-finain Hausa, kuma ya shiga jerin sabbin masu riƙe muƙamai da shugabannin hukumomi.

Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana jerin sabbin naɗe-naɗen, ciki har da masana daban-daban da aka naɗa domin yin aiki a ɓangarorin lafiya, ilimi, da sauransu.

Ana sa ran Sani Danja zai mayar da hankali wajen bunƙasa harkokin matasa da wasanni a Jihar Kano.

Wannan naɗin ya fara aiki nan take, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra