Abba ya buƙaci sabbin Kwamishinoni su cika muradun Kanawa
Gwamnan ya ce dole ne sabbin hadiman su haɗa kai don ciyar da jihar gaba.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci sabbin kwamishinan da sauran hadiman da ya naɗa da su haɗa kai domin cika muradun Kanawa.
Gwamnan, ya yi wannan kiran ne, bayan da ya bai wa sabbin kwamishinan bakwai, masu ba da shawara na musamman guda 13, da sabbin sakatarorai guda shida takardun kama aiki a wani taro da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano a ranar Litinin.
- Zulum ya sanya hannu kan kasafin 2025 na N615.8bn
- An kashe N2trn kan gyaran lantarki amma kamar an shuka dusa
Sabbin kwamishinonin sun haɗa da Shehu Wada Sagagi a matsayin Kwamishinan Zuba Jari, Kasuwanci da Masana’antu, Dokta Ismail Aliyu Danmaraya a matsayin Kwamishinan Kuɗi.
Akwai Dokta Shehu Sani a matsayin Kwamishinan Lantarki da Makamashi, da Dokta Dahiru Hashim a matsayin Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi.
Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Abdulkadir Abdulsalam a matsayin Kwamishinan Ci gaban Karkara, Ibrahim Abdullahi Wayya a matsayin Kwamishinan Tattaunawa, da Wada Ma’aji a matsayin Kwamishinan Sayen Kayan Aikin Gwamnati.
Gwamnan ya buƙaci sabbin jami’an gwamnatin da su yi aiki da gaskiya, inda ya ce dole ne su mayar da hankali a kan buƙatun jama’a.
“Buƙatun al’ummar Kano suna da yawa, kuma dole ne mu haɗa kai don kawo sakamako mai kyau,” in ji shi.
Ya kuma ƙara da cewa, yana so su yi aiki tare da juna domin tabbatar da samar da ingantaccen aiki da goyon bayan manufofin gwamnati.
A cewarsa hakan ya haɗa da inganta ababen more rayuwa, ilimi, lafiya, da ƙarfafa wa mata da matasa, da kuma bunƙasa noma.