Abba ya karrama fitattun Kanawa 35

Bikin ya samu halarcin dattawa da kuma fasihai a fannonin rayuwa daban-daban daga garin na Kano.

Abba ya karrama fitattun Kanawa 35

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karrama wasu mutum 35 ’yan asalin Jihar Kano waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa.

Daga cikin waɗanda gwamnan ya karrama akwai janar-janar ɗin soji 19, Farfesoshi 6 da wasu fitattun Kanawa 10.

Aminiya ta ruwaito cewa, an bayar da lambobin yabon ne ga fitattun mutanen maza da maza a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Kano ranar Asabar da daddare.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce waɗanda suka samu lambobin yabon sun yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa kuma a dalilin haka an samu ci gaba musamman wajen inganta rayuwa da tattalin arzikin Jihar Kano da Nijeriya gaba ɗaya.

Abba ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa gwiwa da waɗannan zaƙaƙurai domin tabbatar da haɗin kai, zaman lafiya da kuma ci gaban Jihar Kano.

Gwamnan ya kuma hori matasa masu tasowa da su ɗauki waɗannan fitattun mutane a matsayin madubi wajen karkatar da alkalar rayuwarsu a fannonin ilimi daban-daban domin ɗaga martabar Kano a nan cikin gida da ƙetare.

Ya miƙa godiyarsa ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudunmawa wajen ganin an samu nasarar gudanar da taron ciki har da Gwamnatin Tarayya ta ba da goyon baya.

Daga cikin waɗanda aka karrama akwai mace ta farko a Arewacin Nijeriya da ta zama Farfesa a fannin likitancin mata da ƙananan yara da mace ta farko a matsayin Kwamishinar ’Yan sanda da kuma Bakano kuma ɗan Nijeriya na farko da ke riƙe da muƙamin Shugaban Ƙungiyar Injiniyoyi ta Duniya.

A nasa jawabin, Shugaban Limaman Nijeriya, Sheikh Nasir Muhammad Adam, ya ƙalubalanci waɗanda aka karrama da su kasance alƙiblar da za ta zama haske ga matasa masu tasowa kafin cikar wa’adinsu a ban ƙasa.

Fitattun Kanawan da aka karrama sun haɗa da Air Marshal Hassan Bala Abubakar, Manjo-Janar M S Ahmed, Manjo-Janar IS Ali, Manjo-Janar A M Garba, Manjo-Janar Sani Sumaila Ibrahim, Manjo-Janar B U Yahya, Manjo-Janar S Y Bashir, Manjo-Janar U B Abubakar, Manjo-Janar Faruk Mijinyawa da Manjo-Janar Jamal Abdulsalam.

Sauran sun haɗa da Air Vice Marshal M Yusuf, Air Vice Marshal G A Bello, Air Vice Marshal B R Mamman, Air Vice Marshal SK Usman, Air Vice Marshal M S Ibrahim, Air Vice Marshal KM Umar, Rear Admiral Abdullahi Ahmad, Rear Admiral Aliyu Gaya da Rear Admiral Idi Abbas.

Ragowar waɗanda suka samu karrramawar sun haɗa da Farfesa Shehu Ahmad Said Galadanci, CON, Dokta Nasiru Sani Gwarzo, Yakubu Adamu Kofar Mata, DIG Dasuki Galadanchi, DDG DSS, Alhaji Ado Muazu, Farfesa Umma Abdullahi, Farfesa Hadiza Galadanci, Farfesa Nazifi Abdullahi Darma, Farfesa Hamisu Armayau Bichi, Farfesa Sagir Adamu Abass da Kwamishinar ’Yan sanda, CP Hajiya Hauwa Ibrahim.

Akwai kuma Rislanuddeen Muhammad, Injiniya Mustafa Balarabe Shehu, Arc. Hauwa Hassan Tudunwada, Ado kabiru Minjibir Mni da kuma Marwan Mustapha Adamu mni.

Bikin ya samu halarcin dattawa da kuma fasihai a fannonin rayuwa daban-daban daga garin na Kano.

 

Osimhen ya maka ɗan jarida a kotu

Abba ya karrama fitattun Kanawa 35

Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa

Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu