Abba ya mayar da filin Idi cibiyar harkokin addinin Musulunci

Gwamnan ya sanar da cewar bayan ƙaramar salla a dasa harsashin ginin cibiyar.

Abba ya mayar da filin Idi cibiyar harkokin addinin Musulunci

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin mayar da Filin Idi na Ƙofar Mata zuwa Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa don Harkokin Addinin Musulunci.

Sabuwar cibiyar za ta zama wajen gudanar da taruka da karatuttukan addini maimakon barin filin ana amfani da shi sau biyu a shekara don Sallar Idi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron buɗa-baki da ya shirya a Fadar Gwamnatin jihar a ranar 15 ga watan Ramadan.

Taron ya samu halartar Mambobin Majalisar Malamai, inda suka tattauna kan haɗin kai da kuma rawar da malamai ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya.

Gwamna Abba ya ce za a kafa harsashin ginin cibiyar makonni biyu bayan Sallar Idi Ƙarama, sannan daga bisani za a miƙa ta ga malamai don su kula da ita.

Baya ga haka, gwamnan ya kuma bayyana aniyarsa na gyara dukkanin masallatan Juma’a a faɗin jihar don tabbatar da cewa sun zama ingantattun wuraren ibada.

Ya umarci Kwamishinan Harkokin Addini da ya tattara sunayen masallatan da ke buƙatar gyara cikin gaggawa.

Hakazalika, gwamnan ya kuma sanar da cewa ana gina sabon babban Masallacin Juma’a a Fadar Gwamnatin jihar domin ƙara wa masu ibada wajen da ya fi girma da dacewa.

Da yake jawabi a madadin sauran malamai, Sheikh Muhammad Nasir Adam, limamin Masallacin Sheikh Ahmad Tijjani, ya yaba da hangen nesan gwamnan.

Taron ya samu halartar mambobin Hukumar Shari’a, Majalisar Zartarwa, da wasu manyan baƙi.

Gwamnan ya tabbatarwa da malaman addini cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sauraron shawarwarinsu domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito a Kano.