Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano
Naɗin na zuwa ne watanni biyu bayan sauke tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Dokta Baffa Abdullahi Bichi.
![Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2024/05/Abba-signing.jpg)
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yammacin ranar Asabar.
Sanarwar ta ce naɗin sabon Sakataren Gwamnatin zai fara aiki ne a hukumance daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Fabarairun 2025.
Sanarwar ta ce an naɗa sabon Sakataren Gwamnatin wanda ya shafe sama da shekaru talatin yana aikin gwamnati la’akari da ƙwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban na wajen ganin an cimma muradin gwamnati mai ci na ciyar da Jihar Kano gaba.
Naɗin na Umar Farouk Ibrahim na zuwa ne watanni biyu bayan sauke tsohon Sakataren Gwamnatin Kano, Dokta Baffa Abdullahi Bichi daga muƙamin a sakamakon dalilan rashin lafiya, kamar yadda sanarwar sauke shi ta bayyana haka a baya.