Abba ya nuna damuwa game da gobarar kasuwar Kantin Kwari

Gwamnan ya buƙaci a tsaurara matakai don hana aukuwar irin haka a gaba.

Abba ya nuna damuwa game da gobarar kasuwar Kantin Kwari

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna matuƙar damuwarsa kan gobarar da ta ƙone shaguna da dama a kasuwar Kantin Kwari da ke jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya miƙa sakon jajensa ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa, da kuma al’ummar Kano baki ɗaya.

Ya bayyana lamarin a matsayin babban koma baya ga tattalin arziƙi a jihar.

“Kasuwar Kantin Kwari tubali ce ga tattalin arziƙin Kano, kuma Iftila’in ba iya ‘yan kasuwar ya shafa ba, har da ma jihar,” in ji Gwamnan.

Kazalika, ya yi kira da a ƙara kulawa da tsauraran matakan tsaro don hana aukuwar irin wannan a gaba.

Ya jaddada muhimmancin ɗaukar matakan kariya don kiyaye rayuka da dukiya, inda ya ce kiyaye kasuwar na da muhimmanci wajen ci gaban tattalin arziƙin Kano.

Gobarar ta tashi da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Asabar a Gidan Inuwa Mai Mai da ke kan titin Bayajidda, sannan ta yaɗu zuwa wasu gine-gine da ke cikin kasuwar.

Samun ɗaukin gaggawa daga Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, an samu nasarar kashe wutar.

Gwamna Yusuf, ya yaba wa jami’an kashe gobara, kamfanoni masu zaman kansu, da kuma waɗanda suka taimaka wajen shawo kan gobarar.

Haka kuma, ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki a kasuwar da su mayar da hankali wajen kiyaye matakan kariya don hana faruwar irin wannan lamari a gaba.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta bayar da goyon baya ga ’yan kasuwar da lamarin ya shafa.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya