Abba ya raba wa ƙananan manoma kyautar takin zamani
Majalisar Zartaswar Kano ta amince da sayo takin zamani na sama da Naira biliyan biyar.
A jiya Alhamis ne Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon takin zamani na sama da Naira biliyan daya ga kananan manoma da suka hada da mata da masu bukata ta musamman a jihar.
A wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya raba wa manema labarai, ya ce shirin wani mataki ne na cika alkawarin da gwamnan ya dauka a yakin neman zabe na inganta rayuwa ta hanyar saka hannun jari a harkar noma.
A cewar Sanusi Bature, Gwamnan ya raba takin ne kyauta ga manoman don rage musu radadin halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.
Idan za a iya tunawa Gwamna Yusuf a lokacin yakin neman zabensa a 2023 ya yi alkawarin kawo sauyi a harkar noma ta hanyar samar da ingantattun kayan aikin noma masu arha kamar yadda yake kunshe a cikin kundin manufofinsa da ke shafi na 70 da ya gabatar wa Kanawa mai taken “Alkawarina ga Kanawa.”
Dawakin-Tofa ya bayyana cewa takin zamani samfurin NPK na sama da Naira biliyan daya an raba wa kananan manoma 52,800 a fadin kananan hukumomi 44 , wanda kamfanin samar da kayan noma na jihar Kano (KASCO) ya samar.
Da yake kaddamar da rabon takin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne da nufin rage tsadar kayan noma da kuma bunkasa samar da abinci a Jihar kano.
Ya ce Majalisar Zartaswar jihar ta kuma amince da sayo takin zamani na sama da Naira biliyan biyar wanda nan ba da dadewa ba za a samar wa manoman Kano a farashi mai sauki.
Ya jaddada kudirin gwamnati na ci gaba da samar da abinci ta hanyar samar da taki a kai a kai wanda kamfanin KASCO mallakar jihar zai rika yi.
Ya ce gwamnati na inganta kamfanin KASCO da sauran cibiyoyin masana’antu na jihar don dawo da hanyoyin samun kudaden shiga da kuma dorewar tattalin arzikin jihar.
Wadanda suka samu tallafin da suka hada da mata manoma da masu bukata ta musamman ana sa ran za su samu kilo 25 na takin NPK don tallafa wa ayyukan noma da kuma bunkasa noma don inganta rayuwar al’umma.