Abba ya rage wa maniyyatan Kano kuɗin Hajjin bana

Abba ya yi wa maniyyatan Kano ragin kuɗin ne sakamakon tsadar da kujerar Hajjin bana ta yi.

Abba ya rage wa maniyyatan Kano kuɗin Hajjin bana

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa maniyyatan Jihar Kano ragin kuɗin kujerar Hajjin bana bayan tsadar da ta yi a bayan nan.

Gwamnan ya yi wa maniyyatan da suka riga da biyan kuɗin kujerar bana ragin Naira dubu ɗari biyar bayan ƙarin da Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta yi a makon nan.

Abba ya sanar da yi wa maniyyatan ragin kuɗin ne cikin wani saƙo da ya wallafa wannan Larabar a shafinsa na Facebook.

Ya wallafa cewa, “sakamakon ƙarin kuɗi har kimanin Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari tara (1,900,000) da Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya ta yi a kan kowacce kujerar aikin Hajji, ina farin cikin sanar da dukkanin maniyyatan Jihar Kano cewar Gwamnatin Kano ta musu ragin Naira dubu ɗari biyar (500,000) akan kowacce kujera.

“Wannan ragi da muka samar a yanzu haka na nufin duk wani maniyyaci da ya biya Naira miliyan huɗu da dubu ɗari bakwai (4,700,000) kuɗin babbar kujera da wadanda suka biya Naira miliyan huɗu da dubu ɗari biyar (4,5000,000) kudin karamar kujera za su cika Naira miliyan daya da dubu dari hudu (1,400,000) ne kacal maimakon Naira miliyan ɗaya da dubu dari tara (1,900,000).”

Kazalika, Darakta Janar na Hukumar Alhazan Kano, Alhaji Laninu Danbappa ya yi wa manema labarai karin haske dangane da lamarin.

Alhaji Laninu Danbappa ya bayyana cewa a kiyasin da aka yi Gwambatin Jihar za ta biya kimanin Naira biliyan daya da dubu dari hudu na maniyyatan jihar mutum 2,096.

Danbappa ya jaddada cewa wadanda za su amfana da tallafin su ne maniyyatan da suka biya kudinsu tun da farko na Naira miliyan hudu da dubu dari shida.

“Wadanda za su sami wannan tallafi su ne mutane 2096 wadanda suka riga suka biya kudinsu tun da farko.

“Wadanda kuma suke so su biya a yanzu to za su biya Naira miliyan takwas da dubu kamar yadda Hukumar Aikin Hajji ta Kasa NAHCON ta ayyana.”

Alhaji Laninu ya yi kira ga maniyyatan da su yi kokarin cika kudinsu na Naira miliyan daya da dubu dari hudu kafin cikar wa’adin na gobe Alhamis.

Sai dai ya yi kira ga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa NAHCON da ta roki mahukuntan Saudiyya a kan su kara wa’adin da suka yanke domin ’yan Najeriya masu son tafiya aikin Hajjin su sami damar yin wannan ibadah ta aikin Hajji.

“Ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga Hukumar Aikin Hajji ta Kasa da ta nemi hukumomin kasar Saudiyya su kara mana lokaci yadda maniyyatanmu za su sami damar biyan wannan kudi domin sauke faralli.”

NAHCON ta mayar da kuɗin Hajji kusan Naira miliyan bakwai

A ranar Lahadin da ta gabata ce Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta buƙaci maniyyatan bana da su yi gaggawar biyan N1,918,032.91 ƙari a kan kuɗin kujerar Hajjin bana.

Hukumar wadda ta ce yanzu kuɗin sun koma naira miliyan shida da dubu 800 kan kujera ɗaya, ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin Dala wadda da ita ce ake yin kiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke bukata.

Hukumar ta buƙaci maniyyatan da ke son sauke farali a bana kuma suka riga da bayar da kuɗin ajiya da su gaggauta cika kuɗin daga yanzu zuwa ƙarfe 11:59 na daren 28 ga Maris, 2024.

Hukumar Alhazan ta bayyana cewa ƙarin kuɗin na bayan nan na zuwa saboda lokacin da aka fitar da farashin kujerar aikin Hajjin bana Dalar Amurka ba ta yi tashin da ta yi ba yanzu.

Mai magana da yawun NAHCON, Hajiya Fatima Sanda Usara ta ce hukumar za ta rufe karɓar cikon kuɗin ne a ranar 29 ga watan Maris, kuma daga wannan lokaci babu wani maniyyaci da za su saurara matuƙar bai biya kuɗin kafin lokacin ba.

“Wadanda suka kasa biya suna da zaɓi biyu ko dai su rubuta a mayar masu da kuɗinsu ko kuma su ajiye kudin har zuwa shekara mai zuwa.”

Hukumar ta ce mutum 49,000 ne suka biya kuɗin kujerun a farashin baya daga cikin kujeru 75,000 da Saudiya ta ba mahajjan gwamnati yayin da ’yan kasuwa ke da kujera 20,000 wato masu tafiya ta jirgin yawo.

Saboda haka sanarwar ta ce sabbin waɗanda suke da sha’awar sayen kujerar daga jihohin Adamawa, Borno da Yobe, za su biya Naira miliyan 8,225,467.74 yayin da waɗanda suka fito daga sauran yankunan Arewa za su biya Naira 8,254,464.74.

Haka kuma, sabbin waɗanda ke da sha’awar sauke faralin da suka fito daga yankunan Kudu, za su biya Naira miliyan 8,454,464.74, kuma duk a tsukukun wa’adin rufe karɓar kuɗin da Hukumar NAHCON ta bayar.

Ana iya tuna cewa, tun a watan Fabarairun da ya gabata ne hukumar alhazan ta ƙayyade kusan naira miliyan biyar a matsayin kuɗin kuejrar hajjin bana.

Sai dai tun bayan lokacin, hukumar ta soma tababar ƙara wa maniyyatan kuɗi a dalilin tsadar Dala da ke neman hana yi wa maniyyatan dawainiyar da aka saba yi musu ta masauki, abinci da makamantansu.

A wancan lokacin dai, NAHCON ta buƙaci maniyyata daga jihohin Kudancin Najeriya su biya naira miliyan 4,899,000, yayin da maniyyatan Arewa za su biya naira miliyan 4,699,000.

Sai kuma maniyyatan jihohin Yobe da Maiduguri da aka ƙayyade kuɗin kujerarsu a kan naira miliyan 4,679,000.