Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano

Shi ne karo na huɗu cikin ƙasa da shekaru biyu da gwamnan yake faɗaɗa majalisar zartarwa jihar ta Kano.

Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf a wannan Litinin ɗin ya rantsar da sabon Kwamishinan Ma’aikatar Tsarawa da Bunƙasa Gidaje ta Kano, Ibrahim Yakubu Adamu.

Wannan dai shi ne karo na huɗu cikin ƙasa da shekaru biyu ke nan da gwamnan yake faɗaɗa majalisar zartarwa jihar ta Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa gabanin wannan sabon naɗin, Ibrahim Yakubu Adamu shi ne Shugaban Hukumar Tsara Birane ta Kano KNUPDA.

Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Kano, Haruna Isah Dederi ne ya jagoranci rantsar da sabon Kwamishinan da aka gudanar a fadar Gwamnatin Kano.

Da yake jawabi, Gwamnan ya yaba wa sabon kwamishinan wanda ya ba da shaida kan ƙwazo da kuma ƙwarewa haɗi da gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban birnin na Dabo.

Gwamnan ya buga misali da yadda sabon kwamishinan ya jagoranci aikin tsarawa da kuma bunƙasa rukunin gidajen nan na Kwankwasiyya da Amana da Bandirawo waɗanda aka gina a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015 a zamanin gwamnatin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Sabon kwamshinan wanda ƙwararren mai zana gine-gine ne, Gwamnan ya hikaito yadda ya taka rawar gani wajen tsarawa da kuma aiwatar da wasu muhimman ayyukan gine-gine a lokacin da yake Kwamishinan Ayyuka da Gidaje a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

A wani labarin mai nasaba da wannan, Gwamnan ya umarci duk waɗanda suka mallaki gida a rukunin gidaje na Kwankwasiyya ko Amana ko Bandirawo da su tabbatar sun tare nan da watanni uku ko kuma su sanya ’yan haya.